An Sauya Dan Majalisar Tarayyar Kusada/Ingawa: Masu Ruwa da Tsaki Sun Fito da Sabon Dan Takara

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kankia, Kusada da Ingawa, Hon. Abubakar Yahaya Kusada ya rasa damar sake tsayawa takara bayan kwamitin sasanci na APC ya mayar da kujerar zuwa Karamar Hukumar Ingawa.
Arewa Updates ta rawaito cewa, Hon. Abubakar Yahaya Kusada ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook bayan taron kwamitin sasancin fitar da ɗan takarar jam’iyyar APC a yankin.
Ya bayyana cewa kwamitin sasancin karkashin jagorancin Arc. Ahmed Musa Dangiwa ne ya yanke hukuncin cire Kankia da Kusada daga takarar kujerar majalisar tarayyar.
Matakin ya bai wa Karamar Hukumar Ingawa damar fitar da dan takarar APC domin kujerar a zabe mai zuwa.
Tuni al’umma suka fara bayyana ra’ayoyinsu kan matakin a kafafen sada zumunta.