Shugabar ALGON ta Kano da Salisu Yusha’u Sun Yi Watsi da Gayyatar Kwamitin Sasanci na Gwamna Yusuf

Yunkurin sasanci da aka fara domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027 na ci gaba da ɗaukar zafi, yayin da kwamitin da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kafa ya fara ganawa da masu neman takara da masu ruwa da tsaki daga mazaɓun tarayya da na majalisar jiha daban-daban a faɗin jihar.
An kafa kwamitin sasancin ne domin warware korafe-korafen masu neman takara a cikin jam’iyyar All Progressives Congress tare da ƙarfafa haɗin kai gabanin zaɓen 2027.
Hon. Bala Muhammad Gwagwarwa ne ke jagorantar kwamitin, yayin da Farfesa Nura Yaro D-Tofa ke matsayin sakatare.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Hon. Mutari Ishaq Yakasai da tsohuwar Kwamishiniyar Harkokin Mata, Hajiya Zahara’u, da sauran wasu jiga-jigan jam’iyyar.
Tun farko dai Gwamna Yusuf ya umarci duk masu neman takara ƙarƙashin APC da su koma mazabunsu domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki tare da ƙoƙarin cimma matsaya kan ‘yan takarar da za a amince da su, a matsayin matakin farko na sasanci.
Sabon yunkurin sasancin na da nufin samar da haɗin kai tsakanin masu neman takara da suka nuna rashin gamsuwa tare da tabbatar da cikakken goyon baya ga nasarar APC a zaɓen 2027.
Ɗaya daga cikin mazaɓun da ke jan hankalin jama’a sosai ita ce mazaɓar tarayya ta Doguwa/Tudun-Wada, sakamakon takun-sakar siyasa tsakanin ɗan majalisa mai ci, Alhassan Ado Doguwa da kuma Salisu Yusha’u wanda shi ma ke neman kujerar majalisar wakilai.
Rahotanni sun bayyana cewa masu ruwa da tsaki daga yankin sun amince da Hon. Doguwa a matsayin wanda zai tsaya takara a 2027 ƙarƙashin APC, matakin da aka ce Gwamna Yusuf ya amince da shi.
A wani ɓangare na aikinsa, kwamitin sasancin ya gayyaci masu ruwa da tsaki da masu neman takara daga yankin domin tattaunawa a gidan gwamnatin jihar Kano.
Sai dai Shugabar Karamar Hukumar Tudun-Wada kuma Shugabar ALGON ta Jihar Kano, Sa’adatu Salisu Yusha’u tare da mijinta, Salisu Yusha’u, sun yi watsi da gayyatar kwamitin tare da ƙin halartar zaman sasancin.
Duk da rashin zuwansu, Hon. Alhassan Ado Doguwa, wanda ya shafe wa’adi shida yana wakiltar mazabarsa a majalisar wakilai, ya halarci taron sasancin.
Da yake magana kan lamarin, Sakatare na kwamitin, Farfesa Nura Yaro D-Tofa tare da Hon. Mutari Ishaq Yakasai, sun tabbatar da cewa Hajiya Sa’adatu da Salisu Yusha’u ba su halarci taron ba.
Sun bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da gudanar da sasancin a gidan gwamnatin Kano cikin nasara da kwanciyar hankali.
A cewarsu, ya zuwa yanzu kwamitin ya gana da masu neman takara da masu ruwa da tsaki daga sama da mazaɓun tarayya bakwai da kuma mazaɓun majalisar jiha 13 a faɗin jihar.
Masu bibiyar harkokin siyasa sun fara fassara rashin halartar Hajiya Sa’adatu, wadda ke shugabantar ALGON ta Kano, tare da mijinta Salisu Yusha’u, duk da umarnin Gwamna Yusuf na halartar sasancin, a matsayin wani yanayi da ka iya aika saƙonni marasa kyau a cikin jam’iyyar.
Wasu masu sharhi na ganin yin watsi da gayyatar kwamitin na iya zama alamar rashin girmama ƙoƙarin sasanci tare da ƙara jawo hasashen cewa wasu ɓangarorin da ba su gamsu ba za su iya yin aiki da zai kawo cikas ga nasara da haɗin kan APC gabanin babban zaɓen 2027.
Sai dai duk da haka, mambobin kwamitin sasancin sun bayyana kwarin gwiwar cewa tattaunawar da ake ci gaba da yi za ta ƙara ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar tare da tabbatar da tsayuwar daka a matsayin tsintsiya madaurinki ɗaya kafin zaɓe.