Alhazan Jigawa a Makkah Sun Yabawa Na’ima Idris Kitchen Kan Kyakkyawan Tsarin Ciyarwa
Daga Ibrahim Yaro D-Tofa

Alhazan Jihar Jigawa da suka isa birnin Makkah domin gudanar da aikin Hajjin bana sun bayyana gamsuwa da yadda kamfanin Na’ima Idris Kitchen ke gudanar da aikin ciyar da su abinci a ƙasar Saudiyya.
Mahajjatan sun ce suna samun ingantaccen abinci cikin tsafta da kuma akan lokaci, lamarin da ya taimaka musu wajen gudanar da ibadunsu cikin kwanciyar hankali da walwala.
A wata tattaunawa da Ambasada Aliyu Lawal Saulawa ya yi da wasu daga cikin alhazan, mahajjatan sun yabawa kamfanin bisa tsari da kulawar da yake bai wa alhazai ba tare da nuna bambanci ba.
Haka kuma, kamfanin Na’ima Idris Kitchen ya bukaci alhazan da su rika bayyana duk wata shawara ko korafi da suke ganin zai taimaka wajen ƙara inganta tsarin ba su abinci, domin tabbatar da cikakkiyar gamsuwa ga mahajjatan jihar.
Jami’an kamfanin sun bayyana cewa suna bai wa ra’ayoyin alhazai muhimmanci sosai, tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da inganta ayyukansu domin samar da ingantacciyar hidima ga baƙin Allah.
Alhazan sun kuma jinjinawa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa bisa tsare-tsaren da ta shimfiɗa domin kula da jin daɗinsu a ƙasar Saudiyya.
A ƙarshe, sun yi addu’ar Allah Ya saka wa duk masu ruwa da tsaki da alheri tare da ba su ikon ci gaba da yi wa alhazai hidima cikin gaskiya da rikon amana.