Daily Gazette

An Dakatar da nuna Fin ɗin labarina da Manyan Mata da wasu fina-ginai 20

 

Daga Sadiya Bello Audi

A wani mataki na baya-bayan nan na tabbatar da bin ƙa’idojin da ake da su, Hukumar Tace Fina-Finan ta Jihar Kano ta dakatar da wasu fina-finan Hausa guda 22 bisa zarginsu da karya dokar tace fina-finai.

 

Shugaban hukumar Abba El-Mustapha ne ya sanar da dakatarwar da ta fara aiki nan take bayan wani taron gudanarwar hukumar.

 

A cewar Jami’in yada labarai na Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, an saki jerin fina-finan da  abin ya shafa saboda ƙin bin  ka’idojin tantancewar Hukumar.

 

Ya ƙara da cewa hukumar ta dakatar da jerin fina-finan Hausa guda 22 saboda saba wa ka’idojinmu, wadanda suka bukaci a gabatar da dukkan fina-finan don tantancewa kafin a fito fili.

 

fina-finan  da aka dakatar sun haɗa da Dakin Amarya, Mashahuri, Gidan Sarauta, Wasiyya, Tawakkaltu, Mijina, Wani Zamani, Labarina, Mallaka, Kudin Ruwa, Boka Ko Malam, Wayasan Gobe, Rana Dubu, Manyan Mata, Fatake, Gwarwashi, Jamilun Jiddan, Shahadar Nabila, Dadin Kowa, Tabarmar, Kishiyata, da kuma Riga.

 

Ya kuma  “Dokar ta baiwa hukumar ikon tace duk fina-finan da aka yi niyya don shiryawa, tallata,  ko yada labarai, tare da daidaita duk masu ruwa da tsaki a ciki da wajen jihar Kano.

 

An bai wa furodusoshi da masu shirin da aka dakatar da su wa’adin mako guda su mika ayyukansu ga hukumar.

 

“An umurci furodusoshi da su daina watsa shirye-shiryensu ko yada abubuwan su a talabijin ko dandamali na kan layi, kuma ana sa ran su gabatar da shirye-shiryensu don amincewar tantancewa daga ranar Litinin, 19 ga Mayu, 2025, zuwa Lahadi, 25 ga Mayu 2025,” Sulaiman ya yi gargadin. “Rashin bin wannan doka  zai jawo sakamakon shari’a.”

 

Ya kuma yi kira ga gidajen Talabijin da Hukumar Yada Labarai ta Najeriya (NBC) da su ba da goyon bayan aiwatar da tsarin da kuma taimakawa wajen tabbatar da bin ka’idojin da ke jagorantar masana’antar Kannywood.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top