Daily Gazette

TAKADDAMA TA KUNNO KAI A NDC: TSOFFIN ‘YAN JAM’IYYA SUN KWACE TAKARORI DAGA BANGAREN KWANKWASIYYA A KANO

 

TAKADDAMA TA KUNNO KAI A NDC: TSOFFIN ‘YAN JAM’IYYA SUN KWACE TAKARORI DAGA BANGAREN KWANKWASIYYA A KANO

Daga Ibrahim Yaro D-Tofa

Wata sabuwar takaddama ta kunno kai a jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a Jihar Kano bayan da tsoffin mambobin jam’iyyar suka kwace wasu takarorin majalisun dokoki daga hannun ‘yan bangaren Kwankwasiyya, lamarin da ke nuna alamun rikicin cikin gida gabanin babban zaɓen 2027.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga zargin da tsoffin mambobin jam’iyyar suka yi na cewa ba a mutunta yarjejeniyar rabon mukamai da takarori da aka cimma tsakanin shugabannin NDC da sabbin mambobin da suka shiga jam’iyyar tare da jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Tun bayan shigar Kwankwaso cikin NDC, an cimma yarjejeniyar rabon mukamai da takarori bisa kaso 60 zuwa 40, inda bangaren Kwankwasiyya zai samu kashi 60 cikin 100, yayin da tsoffin mambobin NDC za su rike kashi 40 cikin 100.

Sai dai bayan kammala zaɓen cikin gida ta hanyar sasanci da fitar da sunayen ‘yan takara, tsoffin mambobin jam’iyyar sun sake tada ƙorafin cewa an ware su daga tsarin rabon takarorin, tare da zargin cewa bangaren Kwankwasiyya ya mamaye kusan dukkanin kujerun da aka amince a raba.

Sakamakon haka, shugabancin NDC a Kano ya amince da sauye-sauye da suka shafi wasu kujerun Majalisar Wakilai da na Majalisar Dokokin Jiha, inda aka kwace kujeru biyar na Majalisar Wakilai da kuma kujeru bakwai na Majalisar Jiha daga hannun wadanda ake dangantawa da bangaren Kwankwasiyya tare da mayar da su ga tsoffin mambobin jam’iyyar.

Wata takarda da shugaban NDC na Kano, Alhaji Hussaini Isa Mairiga, ya sanya wa hannu ta tabbatar da sauye-sauyen, inda aka bayyana sababbin sunayen ‘yan takarar da za su wakilci jam’iyyar a wasu mazabu daban-daban na jihar.

Mai magana da yawun NDC a Kano, Ibrahim Waya, ya bayyana cewa sun yi ta kokarin jawo hankalin bangaren Kwankwasiyya kan matsalar amma ba a saurare su ba.

Ya ce jam’iyyar ba ta ma samu cikakken kaso 40 cikin 100 da aka amince da shi ba, yana mai gargadin cewa har yanzu suna da niyyar kwato wasu karin kujeru domin cike gibin da suke ganin an yi musu.

A cewarsa, idan ba a samu maslaha ba, rikicin na iya fadada har ya shafi kujerun Sanata da sauran mukaman siyasa da ke hannun bangaren Kwankwasiyya.

Sai dai bangaren Kwankwasiyya ya yi watsi da zarge-zargen, inda mai magana da yawunsa, Habibu Saleh Mohammed, ya bayyana cewa an tafiyar da dukkan bangarorin cikin tsarin zaɓen fidda gwani kuma an cimma matsaya ta hanyar sasanci.

Ya ce abin mamaki ne a ce bayan kusan kwanaki goma da kammala zaɓen cikin gida ne ake sake tayar da irin wannan batu, yana mai jaddada cewa bangarensu na ci gaba da nazarin lamarin kafin yanke mataki na gaba.

Ana tunanin wannan sabon rikici na iya zama babban kalubale ga haɗakar siyasar da ta samar da tikitin haɗin gwiwa tsakanin Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a zaɓen 2027.

Masanin kimiyyar siyasa, Dakta Kabiru Sa’id Sufi, ya yi gargadin cewa idan ba a gaggauta warware matsalar ba, za ta iya raunana ƙarfin jam’iyyar a Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

A cewarsa, Kano na daga cikin manyan ginshiƙan siyasar NDC a Arewacin Najeriya, kuma duk wani rikici ko ficewar mambobi daga jihar zai iya yin tasiri kai tsaye ga nasarar tikitin Obi-Kwankwaso a babban zaɓen 2027.

Yayin da jam’iyyar ke ƙoƙarin sasanta rikicin, masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa yadda shugabannin NDC da bangaren Kwankwasiyya za su tafiyar da wannan sabani ne zai tantance makomar haɗakar siyasar da ta ja hankalin al’ummar Najeriya gabanin zaɓen 2027.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top