GARO YA JAJANTA WA IYALAN ALHAJI AUDU MANAGER, YA CE RASUWARSa GAGARUMIN RASHI NE GA AL’UMM

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan fitaccen ɗan kasuwa kuma jigo a harkokin ci gaban al’umma, Alhaji Audu Manager, wanda Allah Ya yi wa rasuwa kwanan nan.
Ziyarar ta Garo na daga cikin matakan nuna alhini da jajantawa iyalan mamacin tare da al’ummar da suka amfana da gudummawar marigayin a tsawon rayuwarsa. A yayin ziyarar, Mataimakin Gwamnan ya bayyana rasuwar Alhaji Audu Manager a matsayin babban rashi ba ga iyalansa kaɗai ba, har ma ga al’ummar Kano baki ɗaya, la’akari da irin gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da ci gaban jama’a.
Alhaji Murtala Sule Garo ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, abokansa da duk masu alaka da shi, yana mai addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yalwata masa rahama, Ya sanya Aljannatul Firdaus ta zama makomarsa.
Hakazalika, ya roƙi Allah Ya ba iyalan mamacin, ‘yan uwansa da daukacin masoyansa haƙuri, juriya da ƙarfin guiwar jure wannan babban rashi da ya girgiza zukatan al’umma.
Mataimakin Gwamnan ya tunatar da cewa mutuwa haƙiƙa ce da kowane rai zai dandana, inda ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da yi wa marigayi addu’a tare da kyautata ayyukan alheri domin amfaninsa.
Iyalan marigayin sun nuna godiya matuƙa ga Mataimakin Gwamnan bisa wannan ziyara ta ta’aziyya, tare da yaba masa kan kulawa da jajircewarsa wajen kasancewa tare da al’umma a lokutan farin ciki da na alhini.
Ziyarar ta nuna irin kusancin gwamnatin jihar Kano da al’umma, da kuma muhimmancin nuna tausayi da goyon baya ga iyalan da suka rasa masoyansu a lokutan jarrabawa.
Allah Ya jiƙan Alhaji Audu Manager, Ya sa Aljannatul Firdaus ce makomarsa. Amin.