Daily Gazette

YANZU-YANZU: Ambassador Dr, Muhammad Bello Dalha (Commander), ya amsa kiran da Al-ummar jihar kano da suka dade suna yi na Ya fito Takarar Gwamna, zai yi takara a jam’iyyar PDP a 2027, .

YANZU-YANZU: Ambassador Dr, Muhammad Bello Dalha (Commander), ya amsa kiran da Al-ummar jihar kano da suka dade suna yi na Ya fito Takarar Gwamna, Yanzu dai ya fito, zai yi takara a jam’iyyar PDP a 2027, domin ya ceci Al-ummar Jihar kano

 

Commander ya ce lokaci ya yi da ‘yan Kano za su hada kai domin dawo da martabar jihar ta hanyar amfani da dukiya, ilimi da lokaci wajen gina al’umma mai walwala da ci gaba.

 

Ya bayyana cewa idan Allah Ya ba shi damar zama gwamnan Kano, abubuwan da zai fara mayar da hankali a kai sun hada da:

 

Matsalar tsaro da harkar Daba da ta dami al’ummar kano.

 

Yaki da rashin aikin yi.

 

Samar da sana’o’i ga matasa, har da mata.

 

Farfado da harkar ilimi.

 

Tallafa wa ci gaban matasa da marasa karfi.

 

A cewarsa:

 

“Lokaci ya yi da za mu ceci Kano daga durkushewa tare da dawo da martabar jihar mu.”

 

Daga karshe ya yi kira akan Allah ya bashi nasara a zaben da za a yi.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top