Daily Gazette

Anas Danmaliki Ya Tabbatar da Goyon Bayan Gwamnatinsa ga Ci Gaban Babban Asibitin Dawakin Tofa

 

Anas Danmaliki Ya Tabbatar da Goyon Bayan Gwamnatinsa ga Ci Gaban Babban Asibitin Dawakin Tofa

Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Anas Mukhtar Bello Danmaliki, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na bayar da cikakken goyon baya wajen bunƙasa Babban Asibitin Dawakin Tofa domin inganta ayyukan kiwon lafiya ga al’ummar karamar hukumar.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin mambobin Kwamitin Abokan Babban Asibitin Dawakin Tofa ƙarƙashin jagorancin shugabarsu, Hajiya Mairo Mustapha, a wata ziyarar girmamawa da suka kai masa a ofishinsa.

Da yake jawabi, Alhaji Anas Mukhtar Bello Danmaliki ya yaba wa kwamitin bisa jajircewarsa wajen tallafawa ci gaban asibitin da kuma inganta harkokin kiwon lafiya a karamar hukumar. Ya ce irin wannan haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da al’umma na taka muhimmiyar rawa wajen samar da ingantattun ayyukan lafiya.

Ya tabbatar wa kwamitin cewa karamar hukumar za ta ci gaba da ba su cikakken goyon baya tare da haɗa hannu da su wajen aiwatar da shirye-shiryen da za su bunƙasa ayyukan asibitin, inganta kayayyakin aiki da kuma kyautata kulawar da ake bai wa marasa lafiya.

A nata jawabin, Shugabar Kwamitin Abokan Babban Asibitin Dawakin Tofa, Hajiya Mairo Mustapha, ta yaba wa Shugaban Karamar Hukumar bisa kulawar da yake bai wa bangaren lafiya da kuma ƙoƙarinsa na inganta rayuwar al’ummar Dawakin Tofa.

Ta bayyana cewa kwamitin zai ci gaba da aiki tukuru wajen inganta kyakkyawar alaƙa tsakanin ma’aikatan asibiti da al’umma, musamman ‘yan uwan marasa lafiya, domin samar da fahimtar juna, girmama juna da kuma inganta yadda ake ba marasa lafiya kulawa.

Hajiya Mairo Mustapha ta kuma gode wa Shugaban Karamar Hukumar bisa goyon bayan da yake bai wa kwamitin, tare da tabbatar masa da cewa za su ci gaba da haɗa hannu da karamar hukuma, shugabannin asibiti da sauran masu ruwa da tsaki wajen bunƙasa Babban Asibitin Dawakin Tofa domin amfanin al’umma baki ɗaya.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top