Majalisar Wakilai Ta Amince da Ƙudirin Doguwa Kan Gaggauta Gyaran Gadojin Gada Biyu da Yaryasa

Majalisar Wakilai ta Tarayya ta amince da wani ƙudirin gaggawa da ɗan majalisar mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudunwada, Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya gabatar, inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta fara aikin sake gina gadojin Gada Biyu da Yaryasa da suka rushe a kan babbar hanyar Kano zuwa Jos.
Ƙudirin, wanda Doguwa ya gabatar a zaman majalisar a matsayin batu na gaggawar al’umma, ya samu cikakken goyon bayan ‘yan majalisar, sannan Kakakin Majalisar ya tabbatar da amincewarsa ta hanyar ƙuri’ar murya.
Yayin gabatar da ƙudirin, Doguwa ya bayyana cewa rushewar gadojin biyu na ci gaba da jefa rayukan matafiya cikin haɗari tare da kawo cikas ga harkokin kasuwanci da zirga-zirgar ababen hawa tsakanin jihohi.
Ya ce Gadar Gada Biyu da ke ƙofar shiga Dajin Kiyaye Namun Daji na Palgore a Ƙaramar Hukumar Doguwa da kuma Gadar Yaryasa da ke Ƙaramar Hukumar Tudunwada na daga cikin muhimman gadojin Tarayya da ke haɗa Jihar Kano da jihohin Filato, Kaduna, Nasarawa da Benue.
A cewarsa, an gina gadojin ne tun a farkon shekarun 1970 a zamanin mulkin Janar Yakubu Gowon, kuma tsawon sama da shekara hamsin suna taimakawa wajen safarar mutane, amfanin gona da sauran kayayyaki tsakanin jihohin Arewa da sauran sassan Najeriya.
Doguwa ya ce tsufar gadojin, ƙaruwar zirga-zirgar manyan motoci da yawaitar ruwan sama sun haifar da lalacewarsu, yana mai tunatar da cewa babban gyaran ƙarshe da aka yi musu ya kasance ne a zamanin gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta hannun Asusun Petroleum Trust Fund (PTF).
Ya shaida wa Majalisar cewa Gadar Gada Biyu ta rushe a watan Fabrairun 2026, yayin da Gadar Yaryasa ta rushe gaba ɗaya a watan Yunin wannan shekarar, lamarin da ya katse zirga-zirga tare da shafar kasuwanci da rayuwar al’ummomi da dama.
Doguwa ya ce ci gaba da barin gadojin a haka na iya yin illa ga safarar kayan abinci, kasuwanci tsakanin jihohi da kuma rayuwar dubban matafiya masu amfani da hanyar Kano zuwa Jos.
Bayan amincewa da ƙudirin, Majalisar Wakilai ta buƙaci Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta fara aikin sake gina gadojin ba tare da ɓata lokaci ba.
Haka kuma, ta nemi ma’aikatar ta samar da hanyoyin wucin gadi domin rage wahalar matafiya kafin a kammala aikin.
Majalisar ta kuma umurci Kwamitinta kan Ayyuka da ya kai ziyarar gani da ido zuwa wuraren da abin ya shafa tare da tattaunawa da Ma’aikatar Ayyuka kan jadawalin aiwatar da aikin.
Sannan ta bai wa Kwamitin Bibiyar Aiwatar da Ƙudurorin Majalisa umarnin sa ido kan yadda za a aiwatar da wannan matsaya tare da gabatar da rahoto cikin makonni shida.
Ana sa ran wannan matsaya ta Majalisar za ta hanzarta ɗaukar matakin Gwamnatin Tarayya wajen sake gina gadojin Gada Biyu da Yaryasa, waɗanda rushewarsu ta jawo tsaiko ga zirga-zirga, kasuwanci da sauran harkokin tattalin arziki a kan ɗaya daga cikin manyan hanyoyin Tarayya mafi muhimmanci a Najeriya.