Amirul Hajj na Kano Ya Bukaci Kwamitoci Su Kara Zage Dantse Domin Nasarar Hajjin 2026
Daga Ibrahim Yaro D-Tofa, a Makkah,
Amirul Hajj na Jihar Kano kuma Sarkin Gaya, Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya yi kira ga dukkan jami’ai da mambobin kwamitocin da ke gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 da su ƙara zage dantse tare da nuna ƙwazo, sadaukarwa da aiki tare domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana.
Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya bayyana hakan ne yayin wani muhimmin taro da ya gudana a Gida Mai Lamba Daya da ke Makkah a ranar Lahadi, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai, jajircewa da ɗaukar nauyin da aka dora wa kowa domin cimma manufofin aikin Hajjin bana.
Ya bukaci dukkan jami’an da ke da hannu wajen gudanar da aikin Hajji da su yi aiki ba dare ba rana domin tabbatar da samun nasarar da ake fata, yana mai cewa haɗin kai da kyakkyawar mu’amala tsakanin kwamitoci ne ginshiƙin gudanar da ayyukan alhazai cikin nasara.
Amirul Hajjin ya kuma bayyana cewa shugabancin aikin Hajjin Kano na sa ran kowane kwamiti zai sauke nauyin da aka dora masa yadda ya kamata domin tabbatar da cewa alhazan jihar sun samu ingantattun ayyukan jin daɗi a duk tsawon lokacin aikin Hajji.
Da yake nasa jawabin, Mataimakin Amirul Hajj kuma Sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, ya ce babban burin shugabancin tawagar Hajjin Kano shi ne tabbatar da cikakkiyar nasarar aikin Hajjin bana.
Ya bayyana shirye-shiryen Mina da Arfa a matsayin mafi muhimmancin mataki a dukkan ayyukan Hajji, yana mai cewa nasarar waɗannan shirye-shiryen za ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar aikin gaba ɗaya.
Sarkin Karaye ya kuma yi kira ga dukkan kwamitoci da su ƙara ƙarfafa haɗin kai da taimakon juna wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Haka kuma ya umarci shugabannin kwamitoci da su tattara tare da gabatar da cikakkun rahotannin ayyukansu bayan kammala aikin Arfa domin haɗawa cikin babban rahoton gudanar da Hajjin shekarar 2026.
A nasu martanin, shugabannin kwamitoci daban-daban sun tabbatar wa shugabancin Amirul Hajj da cikakken shiri da aniyarsu ta yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana ba tare da wata tangarda ba.
Taron ya ƙare da sabunta alkawarin haɗin kai da aiki tare daga dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da gudanar da Hajjin 2026 cikin nasara ga alhazan Jihar Kano.
Ibrahim Yaro D-Tofa, daga Makkah, Masarautar Saudiyya.