Doguwa Ya Ce Zai Nuna wa Gwamna Abba Shi “Ɗan Halal” Ne Bayan Ganawa da Kwamitin Sasanci na APC
Ibrahim Yaro D-Tofa 
Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun-Wada, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana cewa zai nuna wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, cewa shi “ɗan halal” ne tare da tabbatar da biyayyarsa da mutuncinsa a harkokin siyasa.
Doguwa ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan kammala wata tattaunawa da kwamitin sasanci da shugabannin jam’iyyar APC a Kano suka kafa domin samar da sulhu tsakanin waɗanda aka bai wa tikitin takara da kuma waɗanda ba su samu ba a cikin jam’iyyar.
A yayin hirar da aka yi da shi bayan ganawar, Doguwa ya ce idan lokacin yaƙin neman zaɓe ya yi kuma aka ga lokaci ya kure, babu lallai sai an je Doguwa da Tudun-Wada domin neman kuri’u.
A cewarsa, “Insha Allah, Allah zai kawo masa ita,” yana mai nuna cewa yana da cikakken tasiri da goyon baya a yankinsa wajen tabbatar da nasarar jam’iyyarsa.
Ɗan majalisar ya kuma yi magana kan asalin yankinsa, inda ya jaddada cewa shi cikakken ɗan Tudun-Wada ne, yana mai cewa dukkan takardunsa na haihuwa da na karatu suna ɗauke da sunan Tudun-Wada ba Doguwa ba.
“Ni cikakken ɗan Tudun-Wada ne. Takarduna na haihuwa da na makaranta duk suna ɗauke da Tudun-Wada, ba Doguwa ba,” in ji shi.
Haka kuma, Doguwa ya bayyana cewa ya zaɓi yin shiru kan wasu muhawara da suka biyo bayan rikice-rikicen siyasa saboda girmama shawarar gwamnan Kano da kuma neman zaman lafiya a jam’iyyar.
“Na zaɓi yin shiru duk maganar da aka yi ban ce komai ba, saboda na tabbatar wa Mai Girma Gwamna cewa na ɗauki shawararsa, na rage fushi kuma na yi shiru,” ya bayyana.
Sai dai ya ce duk masu sukarsa ba sa cewa bai iya aikin majalisa ba ko kuma yana zaman kashe wando a majalisa, domin a cewarsa kowa ya san yana taka rawar gani wajen wakiltar al’ummarsa.
“Babu wanda yake cewa ban iya aikin majalisa ba, ko kuma ni mai dumama kujera ne. Abin da kawai suke cewa shi ne na daɗe a kan kujera, a ba wani dama,” in ji Doguwa.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙoƙarin sasanta rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar APC a Kano gabanin zaɓukan 2027.