Budadiyar Wasika ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso .
Don Allah a Gyara Tsarin Jam’iyya Kafin 2027)

Daga Shehu Tijjani Shareef
Assalamu Alaikum Jagora,
Da girmamawa, biyayya, da ƙaunar gaskiya nake rubuto wannan wasiƙa gareka — Jagoranmu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A matsayina na ɗan jam’iyya mai kishin gaskiya, ina roƙonka da zuciya ɗaya ka saurari wannan shawara ta gyara cikin gida, domin saboda kai ne jam’iyyarmu, kuma kai ne ginshiƙin tsarin da muke alfahari da shi.
Lokaci Ya Yi a Gyara Tsarin Jam’iyya
Yayin da muka shiga shirye-shiryen 2027, ina roƙonka da ka tabbatar da sabon tsari na adalci da gaskiya cikin jam’iyya.
Duk wanda yake son takara, a tura shi ya tafi mazabarsa ya nemi goyon bayan jam’iyya da mutanen ƙasa.
Ka kafa ka’idar cewa duk mai neman takara sai ya samu aƙalla 80% na goyon bayan jam’iyya a ƙasarsa, sannan kai Jagora sai ka ƙara masa saura 20%.
Wannan tsarin zai tabbatar da cewa duk wanda ya fito da tikitin jam’iyya, ya fito ne da sahihin tushe — ba da zalunci ko shishshigi ba.
Zai kuma ƙarfafa haɗin kai, ya rage fitina, ya ƙara gaskiya cikin tsarinmu.
A Daina Siyasar “Ungo Je Ka Kai Ne”
Jagora, da gaskiya da ƙauna nake faɗin haka — idan muka ci gaba da barin tsarin “Ungo je ka kai ne”, waɗanda ke lalata jam’iyya yau su ne za su fi lalata ta gobe.
Suna cutar da kai, suna cutar da jam’iyya, sannan daga baya sukan dawo su ce wai wani daga Local Government ne yasa suka fadi, bayan kai ne ka ɗaga su sama.
Ka Ƙarfafa Gaskiya da Adalci
Da zarar kowa ya koma ƙasarsa ya nemi jam’iyya ta gaskiya, zai daina sharri, daina makirci, kuma zai tsaya kan gaskiya.
Wannan tsarin zai sa mutane su gina jam’iyya daga ƙasa da ƙauna, ba da tsoron asarar gata ba.
Jagora, wallahi idan ka aiwatar da wannan gyara, jam’iyyar za ta ƙarfafa fiye da da, jama’a za su ƙara amincewa da kai, kuma duk wanda ya fito daga gareka, zai fito da sahihiyar amincewar jama’a.
Allah Ya ba ka hikima, jarumta, da hangen nesa wajen aiwatar da wannan gyara mai muhimmanci.
Muna tare da kai, muna yi maka addu’a, domin kai ne jagoranmu kuma kai