Daily Gazette

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kama mutum biyu da ake zargi ‘yan bindiga ne a Shanonno

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da cafke wasu mutane biyu da ake zargin suna da alaka da ’yan bindiga a garin Faruruwa, karamar hukumar Shanono, tare da ci gaba da kokarin da take na shawo kan matsalar rikici tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Makoda.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da rabawa Manema labarai, inda ya ce an Kama Wadanda ake zargin bayan kai wani samame bisa bayanan sirrin da aka samu daga al’ummar Farin Ruwa, lokacin da suke yunkurin shigowa Kano tare da taimaka wa batagari.

A makon da ya gabata ne al’ummar garin Faruruwa suka koka kan baranazar da yan bindiga daga Jihar Katsina suke yi musu, na Satar Shanu da yunkurin garkuwa da mutane don karbar kudin fansa.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar yankin bisa hadin kan da suke bayarwa a Koda yaushe, inda ya yi Kira ga sauran jama’ar jihar idan sunga wani abu da basu amince dashi ba su yi gaggawar sanarwa a ofishin yan sanda mafi kusa don daukar matakin da ya dace.

Haka zalika, rundunar na ci gaba da aiki tukuru domin magance rikicin manoma da makiyaya a mazabar Barebari dake karamar hukumar Makoda.

Wannan na zuwa ne bayan zaman da area kwamanda mai kula da Dambatta, ACP Mohammed Mani Gwarzo ya jagoran ta, kuma Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, ya kira wani taro da masu ruwa da tsaki, a shelkwatar rundunar don daukar matakan da za su tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

CP Bakori ya tabbatar wa da jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace don kare rayuka da dukiyoyi al’umma a fadin jihar Kano.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top