Shugaban Karamar Hukumar D-Tofa Ya Yabawa Sanata Barau Kan Gina Asibitin kwanciya Dawanau
D Shugaban Karamar Hukumar D-Tofa, Alhaji Anas Mukhtar Bello Danmaliki, ya yabawa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, bisa kafa harsashin gina Asibitin Cottage a garin Dawanau, yana mai bayyana aikin a matsayin babban ci gaba da zai inganta harkokin kiwon lafiya a yankin.
Alhaji Anas Danmaliki ya bayyana cewa wannan babban aiki zai amfani al’ummar Dawanau da kuma mazauna garuruwan da ke makwabtaka da ita, ciki har da Tumfafi, Bagadawa da sauran kauyuka da garuruwa da ke yankin Karamar Hukumar D-Tofa.
Ya nuna matuƙar jin daɗinsa da godiyarsa ga Sanata Barau kan wannan gagarumin aikin, yana mai cewa samar da ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya na daga cikin muhimman buƙatun al’umma.
A cewarsa, kammala wannan Asibitin Cottage zai rage wa jama’a wahalar neman kulawar lafiya, tare da rage cunkoso a sauran cibiyoyin kiwon lafiya da ke yankin.
“Wannan shi ne irin aikin da al’umma ke sa ran gani daga gwamnati da wakilan da suka zaɓa. Muna matuƙar farin ciki da godiya ga Sanata Barau Jibrin bisa kawo mana wannan muhimmin aikin da zai amfani dubban jama’a,” in ji Danmaliki.
Ya ƙara da cewa aikin ya nuna irin jajircewar Sanata Barau wajen samar da ayyukan ci gaba da ke taɓa rayuwar al’umma kai tsaye, musamman a fannin kiwon lafiya da walwalar jama’a.
Shugaban karamar hukumar ya bayyana Asibitin Cottage din a matsayin wani muhimmin aiki da zai taimaka wajen bunƙasa harkokin kiwon lafiya, inganta rayuwar al’umma da kuma haɓaka ci gaban tattalin arziki a yankin D-Tofa.
Alhaji Anas Danmaliki ya sake tabbatar da godiya da goyon bayan al’ummar Karamar Hukumar D-Tofa ga Sanata Barau Jibrin, tare da bayyana fatan ganin an kammala aikin cikin lokaci domin amfanin jama’a.