MATSALOLIN AURE BA NA KAFAR SADARWA BA NE — FADILA H. ALIYU

Daga Ibrahim Yaro D-Tofa
Wata mai sharhi kan al’amuran zamantakewa, Fadila H. Aliyu, mamallakiyar shafin Golden Pen a Facebook, ta yi kira ga mata da su guji yada matsalolin aurensu a kafafen sada zumunta, musamman batutuwan da suka shafi cin amanar aure.
A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Facebook, Fadila ta bayyana cewa duk da irin radadi da takaicin da mace ke ji idan ta kama mijinta yana cin amanarta, bai kamata hakan ya zama dalilin fallasa sirrin gida a bainar jama’a ba.
Ta ba da shawarar cewa idan mace ta ga ba za ta iya boye lamarin ba, ya fi dacewa ta nemi mafita tsakanin iyalanta da na mijinta maimakon yada batun a shafukan sada zumunta.
A cewarta, yawaita kawo irin wadannan matsaloli a kafafen sadarwa na iya rage kunya da tsoron aikata laifin ga wasu masu irin wannan dabi’a, domin idan abu ya zama ruwan dare a idon jama’a, yana iya rasa tasirin da yake da shi a matsayin abin kunya.
Fadila ta kuma jaddada cewa cin amanar aure ba sabon abu ba ne a cikin al’umma, kuma ba yau aka fara fuskantarsa ba. Sai dai ta ce mafita tana cikin gyaran hali, tsoron Allah da kuma mutunta alkawuran aure.
Ta kara da yin kira ga maza da su guji mu’amalar rashin da’a ta hanyar sakonnin waya ko kafafen sada zumunta, tana mai tunatar da su cewa ko da mutum ya goge abin da ya aikata a duniya, akwai hisabi a wurin Allah Madaukakin Sarki.
A karshe, ta yi addu’ar Allah Ya shiryar da ma’aurata, Ya kare gidajen aure daga rikice-rikice, Ya kuma sanya zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’umma baki daya.