Ranar Yara ta Duniya: Gwamna Yusuf Ya Sake Jaddada Kudurinsa na Samar da Dama da Makoma Mai Haske ga Kowane Yaro a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na tabbatar da cewa kowane yaro a fadin jihar ya samu damar ilimi, kiwon lafiya da kariya domin gina makoma mai haske da cike da fata.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a sakonsa na bikin Ranar Yara ta Duniya ta 2026, inda ya bayyana yara a matsayin ginshikin ci gaba mai dorewa da kuma shugabannin da za su jagoranci al’umma a nan gaba.
Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya wakilta, ya ce gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da tsare-tsare da shirye-shiryen da suka shafi walwala, ilimi da ci gaban yara domin tabbatar da cewa babu wani yaro da aka bari a baya.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen inganta harkokin ilimi da lafiya, tare da karfafa matakan kare yara da samar da yanayi mai kyau da zai ba su damar bunkasa basira da cimma burinsu.
“Yara su ne tubalin ci gaban kowace al’umma. Don haka gwamnatinmu ta kuduri aniyar samar da duk wani tallafi da yanayi mai kyau da zai bai wa kowane yaro damar samun ilimi mai inganci, kula da lafiya da kuma cimma burinsa,” in ji shi.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin jihar na bai wa yara masu bukata ta musamman kulawa ta musamman, ciki har da yara masu nakasa, yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma wadanda ke fuskantar kalubalen rayuwa iri-iri.
Ya ce ci gaban yara ba nauyin gwamnati kadai ba ne, illa aiki ne da ke bukatar hadin gwiwar iyaye, malamai, shugabannin gargajiya, kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.
A cewarsa, gwamnatin Kano na aiki kafada da kafada da wadannan bangarori domin kawar da duk wani cikas da ke hana yara samun cikakkiyar damar bunkasa rayuwarsu da bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma.
Haka kuma, ya yi kira ga iyaye, masu kula da yara da malamai da su ci gaba da nuna wa yara kauna, kulawa da kyakkyawar tarbiyya tare da samar musu da yanayin da zai taimaka musu wajen samun nasara a rayuwa.
Gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sanya bukatun yara a sahun gaba, yana mai cewa zuba jari a kan yara shi ne hanya mafi dacewa ta tabbatar da makoma mai cike da ci gaba, zaman lafiya da wadata ga jihar Kano.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ci gaba da kare yara tare da ba su damar girma cikin yanayi mai cike da aminci, ilimi da kyawawan dabi’u.