Daily Gazette

June 5, 2026
22:02

Garo Ya Karɓi Lambar Yabo Ta Musamman Yayin da Inuwa Waya da Mahaddatan Alƙur’ani Suka Jaddada Haɗin Kai Domin Ci gaban Kano

 

Garo Ya Karɓi Lambar Yabo Ta Musamman Yayin da Inuwa Waya da Mahaddatan Alƙur’ani Suka Jaddada Haɗin Kai Domin Ci gaban Kano

Daga Ibrahim Yaro D-Tofa

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Murtala Sule Garo, ya karɓi Lambar Yabo ta Musamman daga Ƙungiyar Mahaddatan Alƙur’ani ta Najeriya saboda gudunmawar da yake bayarwa da kuma goyon bayan da ya dade yana bai wa mahaddata da harkokin addinin Musulunci.

An gabatar masa da lambar yabon ne a yayin wata ziyarar ban girma da tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Kano, Alhaji Inuwa Waya, ya jagoranta tare da shugabannin ƙungiyar zuwa ofishin Mataimakin Gwamnan.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ta yanke shawarar karrama Garo ne bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen tallafa wa mahaddatan Alƙur’ani da kuma ƙarfafa harkokin ilimin addini a tsawon shekaru.

Da yake karɓar lambar yabon, Mataimakin Gwamnan ya nuna matuƙar godiyarsa ga Alhaji Inuwa Waya da shugabannin ƙungiyar bisa wannan karramawa da suka yi masa.

Ya bayyana Alhaji Inuwa Waya a matsayin amini na kusa kuma abokin tafiya a ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da ci gaban Jihar Kano a fannoni daban-daban.

A cewarsa, alaƙar da ke tsakaninsu ta samo asali ne tun a shekarar 2021 lokacin da suka fara aiki tare domin bunƙasa ci gaban siyasa, tattalin arziki, addini da zamantakewa a jihar.

Garo ya jaddada cewa ci gaban al’umma ba zai samu ba sai da haɗin kai tsakanin shugabanni, malamai, masu ruwa da tsaki da sauran al’umma, yana mai cewa ci gaban Kano shi ne babban buri da ke haɗa su gaba ɗaya.

Ya kuma tabbatar da kudirin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’umma tare da samar da ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.

A wata ziyarar daban kuma, Mataimakin Gwamnan ya karɓi baƙuncin mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Honarabul Yusuf Aliyu Tumfafi.

Tattaunawar da aka yi ta mayar da hankali ne kan hanyoyin ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyya, bunƙasa zumunci tsakanin masu ruwa da tsaki da kuma inganta alaƙar aiki tsakanin shugabannin jam’iyyar domin ci gaba da samun nasarori a jihar.

Garo ya bayyana cewa haɗin kai, fahimtar juna da aiki tare su ne ginshiƙan ci gaban kowace jam’iyya da gwamnati.

Ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su ci gaba da rungumar siyasar haɗin kai da haɗin gwiwa domin tabbatar da ci gaba da nasarar jam’iyyar da kuma kyakkyawan shugabanci ga al’ummar Kano.

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa wannan lambar yabo da kuma irin ziyarorin da manyan masu ruwa da tsaki ke kai wa Mataimakin Gwamnan na ƙara nuna irin karɓuwa da amincewar da yake samu a tsakanin al’umma da shugabanni a jihar Kano.

Haka kuma, ana kallon Murtala Sule Garo a matsayin jagoran da ke taka muhimmiyar rawa wajen gina gadar haɗin kai tsakanin bangarori daban-daban domin tabbatar da ci gaba da zaman lafiya a Kano.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top