Jirgi na Biyu na Alhazan Kano Ya Tashi Zuwa Jeddah Dauke da Alhazai 558
Jirgi na biyu na maniyyatan Jihar Kano domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Malam Aminu Kano zuwa Filin Jirgin Sama na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah, ƙasar Saudiyya, dauke da jimillar alhazai 558.
Yayin bikin bankwana da maniyyatan, Amirul Hajj na Hajjin shekarar 2026 kuma Sarkin Gaya, Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya yi wa maniyyatan jawabi inda ya buƙace su da su kasance jakadu nagari na Jihar Kano a duk tsawon zamansu a ƙasa mai tsarki.
Ya tunatar da su muhimmancin kare martaba da mutuncin Jihar Kano ta hanyar kyawawan ɗabi’u da mu’amala mai kyau da juna da sauran al’umma. Haka kuma ya ƙarfafa musu gwiwa da su maida hankali sosai wajen gudanar da ibadu da zarar sun isa birnin Madina, yana mai jaddada alfarmar birnin a matsayin wurin da Annabi Muhammad (S.A.W) yake kwance.
Sarkin Gaya ya kuma shawarce su da su guji hayaniya da gardama marasa amfani tare da mutunta juna, la’akari da girman tafiyar ibadar da suka fito domin gudanarwa.
Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya kare su, Ya ba su lafiya da nasarar gudanar da aikin Hajji tare da dawo da su gida lafiya domin sake haɗuwa da iyalansu da al’ummar Musulmi baki ɗaya.
Taron bankwana da maniyyatan ya kasance wata muhimmiyar dama ta ƙara jaddada bin ƙa’idoji da dokokin aikin Hajji tare da bayar da umarni na ƙarshe ga maniyyatan kafin tafiyarsu.
“Yayin da muke yi wa maniyyatanmu bankwana zuwa wannan tafiya mai albarka zuwa ƙasar Saudiyya, ina kira gare ku da ku mutunta dokoki da ƙa’idojin ƙasar da za ku je,” in ji shi.
Jirgi na biyu ya ƙunshi maniyyata daga ƙananan hukumomi takwas na Jihar Kano da suka haɗa da:
Nasarawa
Tarauni
Kano Municipal
Kumbotso
Rano
Kibiya
Bunkure
Dawakin Kudu
Kamfanin jirgin sama na Max Air ne ya gudanar da jigilar, inda jirgin ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 5:42 na yamma.