Kwamitin Bangajiya da Godiya na Gawuna-Garo Ya Gudanar da Taron Saukar Alƙur’ani da Addu’o’i na Musamman don Tunawa da Marigayi Aminu Dantata

Kwamitin Godiya da Bangajiya na Gawuna-Garo ya shirya wani babban taron saukar karatun Alƙur’ani mai girma da addu’o’i na musamman a ranar Asabar 26 ga watan Yuli domin tunawa da addu’a ga marigayi Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata, da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Dala, Mahmoud Sani Madakin Gini da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Wudil, Abubakar Abdullahi Likita, da kuma marigayi Sheikh Malam Abdullahi Muhammad Yankaba, tare da sauran ‘yan uwa Musulmi da suka rigamu gidan gaskiya.
An gudanar da wannan taro ne a Masallacin da ke kallon gidan Mai Girma Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, a unguwar Miller Road da ke Rukunin Bompai da ke Kano. Taron ya samu halartar al’ummar Musulmi daga sassa daban-daban na jihar Kano da ma wajenta, wadanda suka taru domin yin addu’a da roƙon rahamar Allah ga rayukan marigayun.
A cewar mai taimakawa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna kan harkokin yaɗa labarai, Abubakar Musa DK, “ yayin taron malamai da dama sun gabatar da karatun Alƙur’ani da kuma gabatar d rahama a addu’o’in neman gafara da ga wadanda suka mutu.
Ya ƙara da cewa, “Allah Ya gafarta musu, Ya kuma saka da alheri ga dukkan wadanda suka halarta da waɗanda suka yi fatan alheri a gare su. Amin.”
Taron ya kasance wani ɓangare na ci gaba da nuna godiya da tunawa da ayyukan alheri da gudunmawar da marigayun suka bayar ga al’umma kafin rasuwarsu.