Daily Gazette

June 5, 2026
23:52

Amirul Hajj na Kano Ya Bukaci Alhazai Su Ci Gaba da Hakuri Yayin da Suke Jiran Komawa Gida

 

Amirul Hajj na Kano Ya Bukaci Alhazai Su Ci Gaba da Hakuri Yayin da Suke Jiran Komawa Gida

Daga Ibrahim Yaro D-Tofa

Makkah, Saudiyya – 4 ga Yuni, 2026

Amirul Hajj na Jihar Kano kuma Sarkin Gaya, Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya bukaci alhazan jihar da su ci gaba da nuna hakuri yayin da suke jiran jigilar su zuwa Najeriya bayan kammala aikin Hajjin bana na shekarar 2026.

Amirul Hajj din ya yi wannan kira ne yayin ziyarar da ya kai otal-otal da  daum alhazan Kano  ke zaune a birnin Makkah domin duba halin da suke ciki tare da sauraron koke-kokensu da kalubalen da ka iya tasowa.

A yayin ziyarar da ya kai gidaje na 4 da 5, Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya bayyana cewa duk da an kammala muhimman ibadun Hajji cikin nasara, har yanzu akwai bukatar alhazai su ci gaba da nuna hakuri da juriya har zuwa lokacin da za a fara jigilar su zuwa gida.

Ya ce, “Mun zo ne domin mu gana da ku kai tsaye. Na san daya daga cikin matsalolin da aka gabatar mana ita ce ta sufuri zuwa Masallacin Harami, amma yanzu an magance matsalar domin an samar da motocin da za su rika yi wa alhazai hidima a kowanne masauki.”

 

Ya kara da cewa Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano tana ci gaba da tuntubar Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) domin tabbatar da an gudanar da jigilar alhazai cikin sauki da kuma kauce wa jinkiri.

Amirul Hajj din ya kuma yi kira ga alhazai da su ci gaba da yi wa Jihar Kano da Najeriya addu’o’in zaman lafiya, hadin kai da ci gaba mai dorewa.

A nasa jawabin, Mataimakin Amirul Hajj kuma Sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Muhammad Maharaz, ya bayyana wannan zagayen ziyara a matsayin wani muhimmin mataki da aka fara a wannan shekarar domin kara kusantar shugabannin tawagar Hajji da alhazai.

Ya bukaci alhazai da su kara hakuri yayin jiran jadawalin tashin jiragensu, tare da ci gaba da yi wa kasa addu’a musamman a daidai lokacin da harkokin siyasa ke kara daukar hankali gabanin zabuka masu zuwa.

Hakazalika, wakilan malamai, Sheikh Abubakar Kandahar da Sheikh Tijjani Bala Kalarawi, sun yi wa alhazai wa’azi a gidaje na 4 da 5 daban-daban, inda suka tunatar da su falalar Hajji karbabbe da kuma muhimmancin hakuri, godiya da kyawawan dabi’u yayin zamansu a Kasa Mai Tsarki.

Ziyarorin na daga cikin kokarin da tawagar Hajjin Jihar Kano ke yi na tabbatar da jin dadin alhazai da walwalarsu tare da kula da bukatunsu har zuwa lokacin da za su dawo gida Najeriya cikin koshin lafiya.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top