Alhazan Kano Sun Yaba da Ayyukan Na’ima Idris Kitchen a Makkah

Daga Ibrahim Yaro D-Tofa, Makkah
Alhazan Jihar Kano da ke zaune a Gida na Shida a Birnin Makkah sun bayyana gamsuwarsu da irin hidimar ciyarwa da kamfanin Na’ima Idris Kitchen ke samar musu a yayin gudanar da aikin Hajjin bana.
Alhazan sun ce kamfanin na ba su abinci iri-iri da ya dace da bukatunsu, tare da tabbatar da cewa ana kai musu abincin a kan lokaci ba tare da jinkiri ba.
A zantawarsu da Ambasada Aliyu Lawal Saulawa, wasu daga cikin alhazan sun bayyana farin cikinsu kan yadda kamfanin ke gudanar da ayyukansa cikin tsari da kwarewa.
Sun musamman yaba da yadda jami’an kamfanin ke bibiyar tsarin rabon abinci da kuma tabbatar da inganci da tsaftar abincin da ake bai wa alhazai a kullum.
Alhazan sun ce wannan kulawa ta taimaka wajen kara musu kuzari da natsuwa domin mayar da hankali kan ibadunsu a kasa mai tsarki.
Sun kuma yi addu’ar Allah Ya saka wa masu gudanar da kamfanin da alheri, tare da fatan ci gaba da irin wannan kyakkyawar hidima ga alhazai a nan gaba.
Alhazan Kano da ke Gida na Shida a Makkah sun yaba da inganci, tsafta da kuma isar da abinci a kan lokaci da kamfanin Na’ima Idris Kitchen ke yi yayin aikin Hajjin 2026.