Amirul Hajj Ya Yaba da Ingancin Ayyukan Naima Kitchen a Makkah

Daga Ibrahim Yaro D-Tofa, Makkah
Amirul Hajj na Jihar Kano kuma Sarkin Gaya, Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya yaba da matakan tsafta da ingancin ayyukan da ake gudanarwa a cibiyar girke-girke ta Naima Kitchen da ke birnin Makkah, wadda ke samar da abinci ga dubban alhazan Kano da ke gudanar da aikin Hajjin bana.
Sarkin Gaya ya bayyana hakan ne bayan wata ziyarar bazata da ya jagoranta tare da jami’an Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kano zuwa cibiyar domin duba yadda ake shirya da kuma rarraba abincin da ake kai wa alhazan jihar.
A yayin ziyarar, tawagar ta zagaya sassan girki, wuraren shirya abinci da ma’ajiyar kayan abinci, inda suka ga yadda ma’aikatan cibiyar ke gudanar da ayyukansu tare da bin ƙa’idojin lafiya da tsafta.
Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan kammala ziyarar, Amirul Hajj ya ce manufar ziyarar ita ce tabbatar da cewa alhazan Kano suna samun abinci mai inganci kuma wanda aka shirya cikin tsafta.
Ya ce abin da suka gani ya nuna cewa kamfanin ya tanadi dukkanin matakan da suka dace wajen tabbatar da lafiya da walwalar alhazan jihar.
“Mun zo ne domin ganin yadda ake shirya abincin da ake bai wa alhazanmu. Mun gamsu da matakan tsafta da ingancin ayyukan da muka gani a nan,” in ji Sarkin Gaya.
Tun da farko, Babban Jami’in Gudanarwa kuma Manajan Daraktan Kamfanin Da’am Al Mawasem, Alhaji Nuhu Idris Saleh Fallata, ya bayyana cewa kamfanin ya samar da kayan aiki na zamani da wuraren adana kayan abinci domin tabbatar da gudanar da ayyukan ciyarwa cikin nasara.
Ya kuma ce an yi ƙoƙari wajen samar da nau’ikan abincin da alhazan Kano suka saba da su domin su samu sauƙin gudanar da ibadunsu ba tare da wata matsala ba.
Amirul Hajjin ya yi kira ga masu gudanar da cibiyar da su ci gaba da kiyaye wannan kyakkyawan matsayi har zuwa ƙarshen aikin Hajjin bana, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen ƙara wa alhazan Kano jin daɗi da walwala a ƙasa mai tsarki.