Daily Gazette

 LABARI da Dumi Dumi: ’Yan Bindiga Sun Sace Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi a Garin Bagudu

LABARI da Dumi Dumi: ’Yan Bindiga Sun Sace Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi a Garin Bagudu 

Daga Sani Dutsinma
Bagudu, Jihar Kebbi | Juma’a, 31 ga Oktoba, 2025

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Alhaji Samaila Bagudu, a gidansa da ke karamar hukumar Bagudu da misalin ƙarfe 8:00 na dare, bayan ya kammala sallar Isha’i a masallacin unguwarsu.

Wani mazaunin yankin da ya tattauna da Radio Nigeria a Birnin Kebbi ya bayyana cewa, ’yan bindigar sun iso cikin mota, suka jira lokacin da Mataimakin Kakakin ya fito daga masallaci, suka umarce shi da ya shiga motar da suka zo da ita.

Shaidun gani da ido sun ce ’yan bindigar sun yi harbi a sama domin tarwatsa jama’a kafin su tsere da shi.

“Sun harbi wani yaro a ƙafarsa lokacin da yake ƙoƙarin saka wa Mataimakin Kakakin takalmi,” in ji mazaunin yankin. “An garzaya da yaron asibiti, kuma babu wanda ya rasa ransa a harin.”

Kokarin samun bayanin hukumomin ’yan sanda ya ci tura, domin Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi bai amsa kiran waya ko saƙon WhatsApp da aka tura masa ba.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun fara bin sawun masu garkuwar, amma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wani cikakken bayani daga hukumomi.

Cikakkun bayanai na tafe…

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top