Daily Gazette

Shugaban Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa Ya Rabawa Sakataren Scholarship da Shugaban Kwamitinsa Sabbin Babura

 

Shugaban Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa Ya Rabawa Sakataren Scholarship da Shugaban Kwamitinsa Sabbin Babura

Shugaban Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, Hon. Anas Mukhtar Bello Danmaliki, ya sake jaddada aniyarsa ta inganta ayyukan gwamnati a matakin ƙaramar hukuma ta hanyar ƙarfafa gwiwar ma’aikata da masu gudanar da shirye-shiryen ci gaban al’umma.

A wani mataki da ke nuna jajircewarsa wajen samar da yanayin aiki mai kyau, shugaban ya bai wa Sakataren Scholarship na Ƙaramar Hukumar, Adamu Muhammad Bello, da Shugaban Kwamitin Scholarship, Abdullahi Mujin Yawa, sabbin babura domin taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu cikin sauƙi da inganci.

Wannan tallafi na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Hon. Anas Mukhtar Bello Danmaliki na samar da kayan aikin da za su ƙara wa jami’anta ƙwarin gwiwa, tare da tabbatar da cewa ayyukan da suka shafi ci gaban ilimi da jin daɗin al’umma suna gudana yadda ya kamata.

Masu lura da al’amuran ƙaramar hukumar sun bayyana wannan mataki a matsayin wata alama ta shugabanci nagari da ke daraja sadaukarwar ma’aikata, tare da ba su damar gudanar da ayyukansu cikin inganci da sauri.

Al’ummar Dawakin Tofa sun yaba da wannan kyakkyawan tsari, suna masu fatan Allah Maɗaukakin Sarki Ya ci gaba da ba Shugaban Ƙaramar Hukumar lafiya, hikima da ikon aiwatar da manufofin da za su ƙara bunƙasa ƙaramar hukumar da kuma kyautata rayuwar al’ummarta.

1 thought on “Shugaban Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa Ya Rabawa Sakataren Scholarship da Shugaban Kwamitinsa Sabbin Babura”

  1. I so much respect the leadership of Hon.Anas Mukhtar Danmaliki the executive chairman Dawakin Tofa local government. In his history of our local Government since it’s inception no any leadership of the local government ever secure admissions of students, pays for their school fees and even give them money for provisions.wallahi what he has done to us we the good people of Dawakin Tofa higly greateful.May Allah rewards him in abundance

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top