Daily Gazette

June 6, 2026
04:02

Saudiyya Ta Rufe Ƙofofin Jamarat Bayan Kammala Ayyukan Hajjin Bana

Saudiyya Ta Rufe Ƙofofin Jamarat Bayan Kammala Ayyukan Hajjin Bana

Hukumomin Ƙasar Saudiyya sun sanar da rufe ƙofofin shiga da fita na wurin Jamarat bayan kammala ayyukan Hajjin bana, lamarin da ke nuna kawo ƙarshen amfani da wurin domin gudanar da ibadar jifan shaidan ta shekarar 1447 Hijira.

Matakin ya biyo bayan kammala jifa da alhazai suka yi a ranakun Tashrīƙ, inda miliyoyin Musulmi daga sassa daban-daban na duniya suka gudanar da ibadar cikin tsari, aminci da kwanciyar hankali.

Jamarat na daga cikin muhimman wuraren ibada da ke Mina, inda alhazai ke gudanar da jifan shaidan a matsayin ɗaya daga cikin muhimman ayyukan Hajji, suna kwaikwayon abin da Annabi Ibrahim (AS) ya yi lokacin da ya yi fatali da waswasin shaidan.

Rufe ƙofofin Jamarat na nuna cewa an kammala wani muhimmin mataki na aikin Hajjin bana, yayin da mafi yawan alhazai ke ci gaba da shirye-shiryen komawa ƙasashensu bayan kammala ibadunsu.

Hukumomin Saudiyya sun ce za su fara ayyukan kula da wurin da kuma nazarin yadda aka gudanar da ayyukan bana domin ƙara inganta shirye-shiryen Hajjin shekara mai zuwa.

A bana, an gudanar da aikin Hajji cikin nasara, inda hukumomin Saudiyya suka samar da ingantattun tsare-tsaren tsaro, lafiya, sufuri da sarrafa taron jama’a, matakan da suka taimaka wajen sauƙaƙa gudanar da ibadun miliyoyin alhazai daga sassa daban-daban na duniya.

Masu lura da harkokin Hajji sun bayyana cewa yadda aka gudanar da zirga-zirgar alhazai a wuraren ibada, musamman a Jamarat, ya nuna irin ci gaban da Saudiyya ke samu wajen amfani da fasaha da tsare-tsaren zamani domin tabbatar da tsaro da jin daɗin baƙin Allah.

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top