W
Wani abu da ke faruwa a wannan zamanin shi ne , za ka ga wasu daga birni sun kauyuka sun dauko yara mata masu kananan shekaru sun kawo su birni da zummar za su rinka yi musu aiki suna biyan su.
Wanda wani bincike ya gano cewa wasu daga cikin wadanda suke dauko yaran nan ba su damu da iliminsu ba, ba su damu da lafiyarsu ba ko kuma uwa uba tarbiyarsu. Abinda suka fi damuwa shi ne , su yi masu aiki. Kuma da zarar sun yi laifi a matsayinsu na mutane to fa hukuncin da ake misu da hantara abin ko kare ba zai ci ba.
Wasu za su ce laifin iyayen yara , eh amma bincike ya gano cewa wasu na amfani da talaucin iyayen yaran ne su kuma dauki alkawarin za su rinka aiko musu da kudi kuma idan yarinya ta isa aure za su yi mata kayan daki , wanda ana samu matsala wajen cika alkawarin.
Abubuwa da dama na faruwa a kan irin wadannan yara da ake kawowa birni don yin aikatau, kama daga yadda yaran gida musamman maza suke kulla abota da su wani lokacin ma har da maigida hankalinsa na karkata ga irin wadan.an yara musamman idan suka fara tasawa. Nasan an kwana da sanin cewa ba a san yawan auren da ‘yan aiki suka kashe ba ko da an fada ko kuma an yi shiru.
Wani abu da su irin wadancan mutane suka kasa ganewa shi ne sun dauko yara daga kauye ba su ba su ilimi da tarbiya ba , sun kuma danka musu kananan ‘ya’yansu su suke kula da su anya babu matsala kuwa?
Idan za ka yi tattauna da wasu daga cikin ‘yan matan da suke yawi a titi a birane akwai irin wadannan yaran da za su birni aiki su saba da jar miya wani dalili ya sa matar gida ta koresu su kuma su ki komawa kauye daga nan su bude sabon babin rayuwa Allah Ya kyauta.
Amma menene ku ke ganin zai kawo saukin wanna hali ?
Mu hadu a comment section.