Daily Gazette

Na’ima Idris Kitchen Ta Samu Lambar Yabo Kan Ingantaccen Abinci Ga Alhazai a Makkah

Na’ima Idris Kitchen Ta Samu Lambar Yabo Kan Ingantaccen Abinci Ga Alhazai a Makkah

Daga Ibrahim Yaro D-Tofa, Makkah

Makkah, Saudiyya – Kamfanin samar da abinci na Na’ima Idris Kitchen ya samu lambar yabo da karramawa bisa gagarumar gudunmawar da yake bayarwa wajen samar da ingantaccen abinci mai ɗanɗanon gida ga alhazai da ke gudanar da aikin Hajji a ƙasa mai tsarki.

 

Kamfanin Sana, wani kamfani na ƙasar Saudiyya da aka ɗora wa alhakin samar da masauki da wasu muhimman ayyuka ga alhazai a Makkah, Mina da Arafat, ne ya karrama Na’ima Idris Kitchen saboda yadda ya nuna ƙwarewa da jajircewa wajen ciyar da alhazai da abinci mai inganci da gamsarwa.

 

An bayyana kamfanin a matsayin ɗaya daga cikin kamfanonin da suka yi abin a yaba musu wajen tabbatar da cewa alhazan da ke ƙarƙashin kulawarsu sun samu abinci mai kyau, tsafta da kuma ɗanɗanon gida, lamarin da ya taimaka wajen sauƙaƙa wa mahajjata zaman su a ƙasa mai tsarki.

 

Kamfanin Na’ima Idris Kitchen na ƙarƙashin jagorancin Sheikh Nuhu Idris Fallata, wanda aka yaba wa bisa kyakkyawan tsarin gudanarwa da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin inganci a dukkan matakan shirya da rabon abinci ga alhazai.

 

Da yake jawabi bayan karɓar lambar yabon, jami’in kamfanin, Ambasada Aliyu Lawal Saulawa, ya bayyana cewa nasarar da aka samu ta samo asali ne daga sadaukarwa da jajircewar ma’aikatan kamfanin tare da kulawar shugabancinsa wajen tabbatar da cewa an yi abin da ya dace a kowane lokaci.

 

Ya ce kamfanin ya ɗauki samar da abinci ga alhazai a matsayin amana, kuma yana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da cewa mahajjata sun samu abinci mai inganci, tsafta da kuma ɗanɗanon da zai sanya su jin kamar suna gida duk da kasancewarsu a ƙasa mai tsarki.

 

Ambasada Saulawa ya kuma gode wa kamfanin Sana bisa wannan karramawa, yana mai cewa hakan zai ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da kyautata ayyukansu da hidimtawa alhazai a Makkah.

 

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top