Gwamnatin Kano Ta Sake Jaddada Kudurinta Na Yaki Da Talauci, Ta Bukaci Kara Hadin Gwiwa Tsakanin Masu Ruwa Da Tsaki

Daga Ibrahim Yaro D-Tofa
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da yaki da talauci ta hanyoyi daban-daban domin inganta rayuwar al’ummar jihar da tabbatar da ci gaba mai dorewa.
Gwamnan, wanda Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Murtala Sule Garo, ya wakilta, ya bayyana hakan ne yayin taron tattaunawa na yankin Arewa maso Yamma kan dabarun dakile talauci da samar da hanyoyin inganta walwala da rayuwar al’umma. Taron ya samu goyon bayan UNICEF da kungiyar tarauyar Turai.
A jawabin da ya gabatar a madadin gwamnan, Garo ya bayyana cewa talauci ba wai rashin kudi kadai ba ne, illa yana kunshe da kalubale da suka shafi rashin ilimi, karancin kula da lafiya, rashin matsuguni mai kyau da kuma karancin hanyoyin samun abin dogaro da kai.

Ya ce gwamnatin Kano tana daukar matakai masu yawa da suka hada da fadada damar ilimi, bunkasa ayyukan yi ga matasa, karfafa tsarin kiwon lafiya da kuma aiwatar da shirye-shiryen tallafa wa marasa galihu domin rage radadin talauci a tsakanin al’umma.
Taron ya samu halartar wakilan UNICEF da Tarayyar Turai, masu tsara manufofi, mambobin kungiyar diplomasiyyar kasashen Turai, shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki da ke da ruwa da tsaki wajen samar da ci gaba mai dorewa da kare muradun al’umma.
Mataimakin gwamnan ya yaba da irin gudunmawar da UNICEF da Tarayyar Turai ke bayarwa wajen bunkasa ci gaban zamantakewa da tallafawa marasa galihu, yana mai cewa irin wannan hadin gwiwa na da matukar muhimmanci wajen cimma manufofin rage talauci da inganta rayuwar jama’a.
Ya kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su kara karfafa hadin gwiwa, musayar dabaru da kirkire-kirkire domin gina ingantaccen tsarin kariyar zamantakewa mai dorewa wanda zai amfanar da kowane bangare na al’umma.
A cewarsa, hadin kai, jajircewa da kyakkyawan tsari ne za su tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ilimi mai inganci, kowane iyali ya samu ingantacciyar kulawar lafiya, yayin da matasa kuma za su samu damar ayyukan yi da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar da kasa baki daya.
Ya jaddada cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da hada hannu da abokan hulda na cikin gida da na kasa da kasa domin tabbatar da cewa manufofin rage talauci sun haifar da sakamako mai amfani ga al’ummar jihar.