Hajji 2026: Gwamnatin Kano Ta Tabbatar da Kula da Lafiyar Alhazai 24 a Saudiyya

Makkah, Saudiyya, Gwamnatin Jihar Kano ta ƙara kaimi wajen tabbatar da jin daɗin alhazanta da ke gudanar da aikin Hajjin bana a Ƙasar Saudiyya, inda ta samar da cikakkun ayyukan kiwon lafiya domin kula da lafiyar mahajjata a duk lokacin da suke buƙata.
Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kano ta kafa cibiyoyin kula da lafiya a otal-otal daban-daban da alhazan jihar ke sauka a biranen Makkah da Madina. An kafa cibiyoyin ne domin samar da kulawar lafiya cikin gaggawa tare da rarraba magunguna da sauran kayan aikin lafiya ga mahajjata ba tare da wani ƙarin kuɗi ba.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban Tawagar Yaɗa Labarai ta Hajjin Jihar Kano ta shekarar 2026, kuma Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamna, Malam Mustapha Muhammad, ya fitar.
Ziyarar da aka kai wasu daga cikin cibiyoyin kula da lafiyar ta nuna yadda likitoci da sauran ma’aikatan lafiya ke gudanar da ayyukansu cikin himma, suna kula da alhazai masu fama da matsalolin lafiya daban-daban da suka haɗa da zazzaɓi, ciwon gaɓoɓi da kuma hawan jini.
Sanarwar ta bayyana cewa Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kano ta tanadi isassun magunguna da kayan aikin lafiya domin tabbatar da cewa duk wani alhaji da ya kamu da rashin lafiya ya samu kulawar da ta dace cikin lokaci.
Da yake yi wa manema labarai ƙarin haske a cibiyar kula da lafiya da ke Gida ta Biyar, jagoran cibiyar, Dakta Ashiru Muhammad Sumaila, ya ce tawagar lafiya tana aiki dare da rana domin tabbatar da lafiyar kowane alhaji daga jihar Kano.
A cewarsa, an samar da likitoci, nas-nas da sauran ƙwararrun ma’aikatan lafiya da ke gudanar da aiki ba tare da yankewa ba domin kula da marasa lafiya da kuma ba su magungunan da suka dace.
“Mun shirya tsaf domin kula da lafiyar alhazai a kowane lokaci. Idan akwai mara lafiya da ke buƙatar kulawa ta musamman ko ƙarin bincike, muna tura shi kai tsaye zuwa manyan asibitoci domin ci gaba da ba shi kulawar da ta dace,” in ji Dakta Ashiru Muhammad Sumaila.
Ya kuma tabbatar da cewa babu ƙarancin magunguna ko kayan aikin lafiya, yana mai cewa an tanadi duk abin da ake buƙata domin tabbatar da walwala da lafiyar alhazan jihar yayin gudanar da ibadunsu.
Matakin ya nuna irin ƙudurin Gwamnatin Jihar Kano na tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana ta hanyar samar da ingantattun ayyukan jin daɗi ga mahajjata. Tun da farko, Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi alƙawarin bai wa alhazan jihar kulawa ta musamman, musamman a fannin kiwon lafiya, yana mai jaddada cewa lafiya ita ce ginshiƙin gudanar da ibada cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kano ta kuma buƙaci mahajjata da su gaggauta sanar da jami’an lafiya duk lokacin da suka ji wata matsala ta rashin lafiya domin samun kulawa cikin sauri da kuma kauce wa rikicewar lamura.
Da wannan shiri da aka tanada, alhazan Kano na ci gaba da gudanar da ibadunsu cikin kwanciyar hankali, tare da samun tabbacin cewa gwamnati da jami’an lafiya suna tsaye tsayin daka wajen kare lafiyarsu a ƙasa mai tsarki.