Daily Gazette

Babban Sakatare a  Bauchi Kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Aikin Hajjin 2026 Ya rasu  a Makkah

Babban Sakatare a  Bauchi Kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Aikin Hajjin 2026 Ya rasu  a Makkah

Gwamnatin Jihar Bauchi da daukacin mahalarta aikin Hajjin 2026 sun shiga jimami sakamakon rasuwar Alhaji Shehu Yahaya Jalam, Babban Sakataren Ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG) kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na aikin Hajjin 2026.

Marigayin ya rasu ne a safiyar Asabar da misalin ƙarfe 2:00 na dare agogon Saudiyya, wanda ya yi daidai da ƙarfe 12:00 na dare agogon Najeriya, a Asibitin Al-Noor da ke Makkah bayan gajeruwar rashin lafiya.

Rasuwar tasa ta faru ne yayin da yake gudanar da muhimman ayyukansa na aikin Hajjin bana, inda yake taka muhimmiyar rawa wajen daidaita harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ga mahajjata da jami’an aikin hajji.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Kwamitin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na aikin Hajjin 2026 ya fitar, an bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen ma’aikacin gwamnati wanda ya yi wa Jihar Bauchi hidima cikin gaskiya da ƙwazo tare da bayar da gagarumar gudunmawa wajen nasarar aikin hajjin bana.

Sanarwar ta yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa kura-kuransa, ya karɓi kyawawan ayyukansa, ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus. Haka kuma ta roƙi Allah ya bai wa iyalansa, abokan aikinsa, da daukacin tawagar aikin Hajjin 2026 haƙurin jure wannan babban rashi.

Marigayi Alhaji Shehu Yahaya Jalam ya kasance mutum mai biyayya, tawali’u da kishin yi wa al’umma hidima. Rasuwarsa ta girgiza mutane da dama tare da jawo saƙonnin ta’aziyya daga jami’an gwamnati, abokan aiki da al’umma a ciki da wajen Jihar Bauchi.

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top