
Daga Amir Abdulaziz
Daga shekara kusan 15 zuwa yanzu, ba wai iya ƙananan hukumomi kawai aka kashe a Jihar Kano ba, an kashe Majalisar Dokoki ta Jiha; Ma’aikatu manya da ƙanana, Jam’iyyun siyasa, Masarautu da sauran sassa masu dafawa domin a sauke nauyin al’umma duk sun mutu.
Bana mantawa a 2002 zuwa 2004, Majalisar Dokoki tana iya hawa dokin na ƙi kan wani abu da gwamna yake so kuma dole ya haƙura. Har a 2011 zuwa 2013, Constituency Projects na ƴan Majalisun jiha kaɗai zai iya sauƙaƙa matsalar lalacewar makarantu da wasu matsalolin. Haka kuma a lokacin, kuna iya kai kukanku na alumma wajen Kwamishina ko wani Daraktan sashe a wata ma’aikata kuma buƙata ta biya. Kai a baya, Hakimi zai iya warware wata babbar matsala a ƙaramar hukumarsa balle kuma Ciyaman. Yanzu fa?
Idan ka ɗauke kujerar Gwamna, kusan babu wani muƙami da za a bugi ƙirji kai tsaye a yi wani abin kirki da shi mai ɗorewa. Aikin da muka sani kansiloli da adbezoji suna yi, yanzu gwamna ne yake yi, magoya bayansa suna tafa masa. Idan ba haka ba, me ya haɗa gwamna da gyara ko ƙera kujerun makarantun firamare ko kuma sayen alli yana rabawa a gidan gwamnati?
Ɗaukar ma’aikata, gwamna; bada jari ga masu ƙuli ƙuli, gwamna; ziyarar makarantu, gwamna; rikicin manoma da makiyaya, gwamna; tattaunawa da ƴan fansho, gwamna; kwashe shara, gwamna; zaɓar shugabannin jam’iyya, gwamna; komai ya tattare. Sai ka rasa ina ainihin ministries da hukumonin da abin ya shafa suke kuma me suke yi?
Wannan dalili shi yasa matsalolin ilimi, tsaro, kiwon lafiya, noma, raya karkara, muhalli, ruwan sha da sauransu kullum suke ƙara taɓarɓrewa tun daga tushe a Arewacin Najeriya. Gwamnatocin Jihohi sun ɗaukarwa kansu wata haɗama da babakere mara amfani. A gefe ɗaya kuma an tare arziki a hannun wasu tsirarun mutane yayin da jama’a suke cikin ƙunci.
Idan gwamnoni sun karɓi maƙudan kuɗi daga Tarayya sai su danƙaresu wajen gina gadojin sama da ƙasa a birane domin burga da rinto. Idan an damesu da ƙorafi, sai su tsakuri kaɗan su yi gyaran makaranta da asibitoci nan da can. Idan an ce basu kyauta ba sai su ce aiyuka sun musu yawa. Bayan kuma sun karɓe aikin kowa sun mayar nasu saboda su kaɗai suka iya kashe kuɗi da bada kwangila, gani suke kowa sakarai ne, ba shi da wayo.
Ita matsalar al’umma haɗuwa ake a kan ta. Idan a haka za a ci gaba da tafiya, abubuwa zasu yi ta taɓarɓarewa koda kuwa a Jihar da gwamnanta ya fi kowa aiki ne da kishin jama’a..
Allah Ya kyauta.
Amir Abdulazeez
31-07-2025