Daily Gazette

Pantami Ta Tsaya Cak, Dubban Jama’a Sun Yi Tururuwar Tarbar Jamil Gwamna

Pantami Ta Tsaya Cak, Dubban Jama’a Sun Yi Tururuwar Tarbar Jamil Gwamna

 

Dubban al’ummar unguwar Pantami da ke birnin Gombe sun fito kwansu da kwarkwatarsu domin tarbar ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC, Dr. Jamil Isyaku Gwamna, a wata ziyara da ta rikide zuwa babban taron siyasa.

 

Ziyarar ta ranar Lahadi ta haɗa maza da mata, matasa da dattawa, inda dandazon jama’ar ya ba da hoton gagarumar tarba ga ɗan takarar, wanda aka fi sani da Sardaunan Gombe.

 

Dr. Gwamna ya kai ziyarar ne domin ƙaddamar da sabon ofishin kamfen na APC a yankin, wanda Alhaji Abdulhamid Jibrin ya buɗe, da nufin ƙarfafa ayyukan yaɗa manufofin jam’iyyar da tattara magoya baya tun daga tushe.

 

Sai dai babban abin da ya ɗauki hankalin jama’a shi ne yadda dandazon al’ummar yankin suka yi tururuwar zuwa wajen taron, lamarin da ya mayar da bikin buɗe ofishin zuwa wani babban taron siyasa da ya nuna farin cikin jama’a da zuwan ɗan takarar.

 

Wasu daga cikin waɗanda suka samu damar yin jawabi sun bayyana goyon bayansu ga Dr. Gwamna, suna mai cewa sun yi imanin shi ne mutumin da ya fi dacewa da jagorancin jihar Gombe.

 

Da yake jawabi, Dr. Jamil Gwamna ya nuna godiya ga al’ummar Pantami bisa irin tarba da karamcin da suka nuna masa, yana mai jaddada muhimmancin hulɗa kai tsaye da jama’a domin fahimtar buƙatunsu da samar da shugabanci mai amfani.

 

Ya kuma jaddada buƙatar haɗin kai tsakanin shugabanni da al’umma wajen cimma muradun ci gaba da inganta rayuwar jama’a.

 

Buɗe ofishin na daga cikin ƙoƙarin APC na faɗaɗa tsarin kamfen ɗinta da ƙarfafa hulɗa da magoya baya a matakin ƙasa, yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

 

 

 

 

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top