Gwamna Abba Yusuf Ya Jinjinawa Na’ima Idris Kitchen Kan Ingantaccen Ciyar da Alhazan Kano a Makkah
Daga Ibrahim Yaro D-Tofa, Makkah
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba da irin ingantaccen aikin da Kamfanin Na’ima Idris Kitchen ke yi wajen samar da abinci mai kyau ga Alhazan Jihar Kano da ke gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da Alhazan Jihar Kano bayan kammala aikin Hajjin bana, inda ya ce tun lokacin da ya isa Makkah yake cin irin abincin da ake tanadarwa Alhazan jihar, lamarin da ya ba shi damar tabbatar da inganci, tsafta da kuma dandanon abincin da kamfanin ke samarwa.
A cewarsa, Na’ima Idris Kitchen ta nuna kwarewa da jajircewa wajen tabbatar da cewa Alhazan Kano sun samu kulawa ta musamman ta fuskar abinci a tsawon zamansu a ƙasa mai tsarki.
“Tun da na zo Makkah, irin abincin da Alhazanmu ke ci shi nake ci. Na gamsu cewa kamfanin Na’ima Idris Kitchen na gudanar da aiki mai inganci kuma ya cancanci yabo saboda yadda yake samar da abinci mai kyau da tsafta,” in ji gwamnan.
Haka kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya kai ziyara kai tsaye wuraren da ake girki da sarrafa abincin Alhazan Kano, inda ya gamsu da matakan tsafta da kuma yadda ake gudanar da aikin cikin tsari da ƙwarewa.
A jawabansu daban-daban, Amirul Hajjin Kano na shekarar 2026, Dr. Ibrahim Aliyu Abdulkadir, da Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Abubakar Ibrahim Matawalle, sun tabbatar da cewa Alhazan jihar na samun wadataccen abinci mai inganci a Makkah, wanda Na’ima Idris Kitchen ke samarwa.
Sun bayyana cewa ingancin abincin da kuma yadda ake isar da shi cikin lokaci ya taimaka wajen samar da walwala da kwanciyar hankali ga mahajjatan Kano yayin gudanar da ibadunsu.
Dangane da shirin dawowar Alhazai gida Najeriya, Gwamna Abba Yusuf ya bukaci mahajjatan da su ci gaba da nuna hakuri da juriya yayin da ake jiran fara jigilar su zuwa gida.
Ya bayyana cewa kamfanin jiragen sama da ke kula da jigilar Alhazan Kano ya sanar da ranar 24 ga Yuni, 2026 a matsayin ranar da za a fara dawo da mahajjatan jihar zuwa Najeriya. Sai dai ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar na ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin duba yiwuwar samun damar fara jigilar Alhazan tun kafin wannan lokaci.
Gwamnan ya gode wa Alhazan Kano bisa kyakkyawan wakilcin da suka yi wa jihar da ƙasa baki ɗaya tare da addu’ar Allah Ya karɓi ibadunsu kuma Ya dawo da su gida lafiya.