Daily Gazette

Engr. Umar Ganduje Ya Kai Ziyarar Jaje da Duban Marasa Lafiya, Ya Nuna Tausayi da Kishin Al’umma

 

Engr. Umar Ganduje Ya Kai Ziyarar Jaje da Duban Marasa Lafiya, Ya Nuna Tausayi da Kishin Al’umma

Daga Ibrahim Yaro D-Tofa

Litinin, 8 ga Yuni, 2026

Babban Darakta a Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Karkara (REA), Engr. Umar Abdullahi Ganduje, FNSE, ya sake nuna kyakkyawan misali na jagoranci mai tausayi da kula da jama’a, inda a ranar Litinin ya kai jerin ziyarce-ziyarce na jaje da duban marasa lafiya domin nuna goyon baya da tausayi ga iyalai da daidaikun mutane da ke fuskantar kalubalen rayuwa.

A yayin ziyarar tasa, Engr. Ganduje ya kai dubiya ga mahaifin Hon. Umar Ishaq (Mai Wayo) wanda ke kwance yana karbar magani a Asibitin Nasarawa. Ya yi masa addu’ar samun lafiya cikin gaggawa tare da fatan Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi cikakkiyar waraka.

Haka kuma, Engr. Ganduje ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Mallam Sani Gilashi Haruna bisa rasuwar ‘yarsa da Allah Ya yi a kwanakin baya. Ya bayyana alhininsa kan wannan babban rashi tare da addu’ar Allah Ya gafarta mata, Ya jikanta da rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarta, sannan Ya ba iyalanta hakurin jure wannan jarabawa.

A ci gaba da ziyarce-ziyarcen, ya kuma kai dubiya ga Hon. Idris Kaugama wanda ke fama da rashin lafiya. Engr. Ganduje ya yi masa addu’ar samun sauki da cikakkiyar lafiya, yana mai rokon Allah Ya yaye masa duk wata damuwa ta rashin lafiya.

Da yake jawabi yayin ziyarce-ziyarcen, Engr. Ganduje ya jaddada muhimmancin kasancewa tare da jama’a a lokutan farin ciki da kuma na jarrabawa, yana mai cewa taimakon marasa lafiya da jajanta wa wadanda suka rasa masoyansu na daga cikin kyawawan dabi’u da addinin Musulunci da al’adunmu suka koyar

.

Ya kuma yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da Ya bai wa marasa lafiya lafiya mai dorewa, Ya gafarta wa mamaciyar, tare da bai wa iyalanta da masoyanta hakurin jure wannan babban rashi.

A ziyarce-ziyarcen, Engr. Ganduje ya samu rakiyar Dr. Junaidu Yakubu Muhammad, Hon. Ahmad Abbas Ladan, da sauran manyan abokai da masu ruwa da tsaki.

Mutane da dama sun yaba da wannan kyakkyawan mataki na Engr. Ganduje, suna mai bayyana cewa hakan wata alama ce ta kusancinsa da al’umma da kuma jajircewarsa wajen raba wa jama’a damuwarsu a lokutan bukata.

Lallai, wannan aiki ya sake tabbatar da cewa nagartaccen shugabanci ba ya tsaya ga gudanar da ofis kawai, har ila yau yana bayyana ne ta hanyar tausayi, jinkai da kasancewa tare da jama’a a lokutan da suka fi bukatar hakan.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top