HAJJI 2026: A Ranar Arfa, Doguwa Ya Bukaci Alhazai Su Yi Wa Najeriya da Gwamnatin Tinubu Addu’a, Ya Yaba da Salon Mulkin Gwamna Abba
Daga Ibrahim Alhaji D-Tofa, Makkah, Masarautar Saudiyya
Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Majalisar Wakilai ta Yankin Arewa (Northern Region Caucus) kuma Shugaban Kwamitin Albarkatun Man Fetur na Majalisar Wakilai (Upstream), Alhassan Ado Doguwa, ya yi kira ga alhazan Najeriya da su yi amfani da falalar Ranar Arfa wajen yi wa Najeriya, shugabanninta da al’ummarta addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa.
Doguwa ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a filin Arfa da ke Makkah a Masarautar Saudiyya, inda miliyoyin Musulmai daga sassa daban-daban na duniya suka hallara domin gudanar da ɗaya daga cikin manyan rukunnan aikin Hajji.
Ya ce Ranar Arfa wata babbar dama ce ga Musulmi domin neman rahama da gafarar Allah, don haka ya kamata alhazan Najeriya su tuna da ƙasarsu a cikin addu’o’insu, tare da roƙon Allah Ya kawo zaman lafiya, tsaro da bunƙasar tattalin arziki.
Doguwa ya kuma buƙaci alhazan su yi addu’a ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin Allah Ya ba ta hikima da nasara wajen gudanar da harkokin ƙasa da inganta rayuwar al’ummar Najeriya.
Ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa da addu’o’i da haɗin kan ‘yan ƙasa, Najeriya za ta shawo kan ƙalubalen da ke gabanta tare da samun ci gaba mai ma’ana a fannoni daban-daban.
Da yake magana kan harkokin Kano, Doguwa ya yaba da salon mulkin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya bayyana a matsayin shugaba mai sauƙin kai kuma mai kusanci da talakawa.
A cewarsa, al’ummar Kano suna da sa’a matuƙa da samun Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ke saukowa zuwa matakin talakawa domin sauraron matsalolinsu da kuma nemo hanyoyin magance su.
“Gwamna Abba Kabir Yusuf shugaba ne mai tausayi da kula da jama’a. Yana tafiyar da mulki ne cikin kusanci da talakawa, kuma hakan ya sa yake samun karɓuwa a zukatan al’umma,” in ji Doguwa.
Ya ƙara da cewa darussan Hajji suna koyar da daidaito da tawali’u, inda kowa yake zama ɗaya ba tare da la’akari da matsayinsa na siyasa ko tattalin arziki ba.
Doguwa ya ce duk lokacin da ya zo Makkah yana haɗuwa da jama’a iri-iri ba tare da nuna bambanci ba, domin a ƙasar Allah babu wani matsayi na musamman.
“A Makkah babu VIP. Kowa da kowa daidai yake a gaban Allah. Wannan shi ne babban darasin Hajji, wanda yake koya wa shugabanni muhimmancin tawali’u da kusanci da jama’a,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su ci gaba da mara wa Gwamna Abba Kabir Yusuf baya tare da sake zaɓensa a wa’adi na biyu a zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa ayyukan ci gaba da salon shugabancinsa sun cancanci a ba shi damar ci gaba da tafiyar da jihar.
A yayin zaman da yake yi a filin Arfa, an ga Doguwa yana musayar gaisuwa da tattaunawa cikin annashuwa da alhazai da baƙi daga sassa daban-daban na Najeriya da ma sauran ƙasashe, lamarin da ya nuna ruhin haɗin kai da ‘yan’uwantaka da Hajji ke koyarwa.
Wasu daga cikin alhazan sun yaba da yadda yake mu’amala da jama’a cikin sauƙi da karamci, ba tare da nuna bambancin matsayi ko muƙami ba.
Daga ƙarshe, Doguwa ya sake jaddada muhimmancin addu’a a wannan rana mai albarka, yana mai kira ga alhazai da su ci gaba da roƙon Allah Ya tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Najeriya baki ɗaya.