An Fara Kiraye-kiraye Da Hon. Abubakar Wada Nas Funtua, Ya Tsaya Takarar Majalisar Dokokin Jiha A 2027 Ya Wakilci Karamar Hukumar Funtua.

Al’ummar ƙaramar hukumar Funtua jihar Katsina, Dattijai, Matasa Da Mata, Sun kiraye-kiraye ga fitaccen matashi, Ɗan Gwagwarmaya Hon. Abubakar Wada Nas Funtua, da ya fito takarar kujerar Majalisar Dokokin Jiha domin wakiltar su a zaɓen shekarar 2027.
Kamar yadda rahotanni daga sassa daban-daban na ƙaramar hukumar Funtua suka riskemu, sun nuna cewa wannan kira na ƙaruwa ne sakamakon yadda matashin ya nuna jajircewa da himma wajen hidimtawa al’umma, tare da nuna kishin ci gaban yankin, tare da tunawa da gudummawar da mahaifinsa ya bada ga cigaban al’ummar jahar Katsina da karamar hukumar funtua da Najeriya.
Masu ruwa da tsaki da dama sun bayyana cewa, Hon. Abubakar Wada Nas ya shahara wajen gudanar da ayyukan alheri, tallafa wa matasa da marasa galihu, da kuma bayar da gudunmawa a fannoni daban-daban na ci gaban al’umma, kamar irin kyawawan halayen mahaifinsa marigayi Alhaji Wada Nas Funtua
Wanda tarihi ya nuna alokacin rayuwar mahaifinshi Duk shekarun da yayi yana hidimar siyasa be taba’ kawo dan’shi Ko wani daga cikin yan’ uwanshi domin ya tsaya takaraba
Sanin kowane mahaifinshi ya bada gudun muwa sosai wajan ganin al’umma sun samu shugabanci na gari bisaga cancanta Batare da nuna bam banci ga ya’yan talakawa ba wajan tsaida shuwagabani wa’anda zasu kawo cigaba ga al’umma
Kamar irin yadda alokacin rayuwarshi ya Jajirce sosai wajan kawo shuwagabani irinsu tsohon shugaban kasa Marigayi Muhammadu Buhari da dai sauran su
A cewar wani mazaunin Funtua ya bayyana cewa “Lokaci ya yi da za’a ba irin waɗannan matasa dama su kawo sauyi mai ma’ana, domin suna da sabbin dabaru da hangen nesa da kuma gogewa sosai wajan nemo aiyukan cigaba ga al’umma musamman matasa” inji shi
Haka kuma, wasu daga cikin shugabannin al’umma sun jaddada cewa, halayen nagarta, gaskiya da rikon amana da matashin ke da su, sun sanya ya zama ɗaya daga cikin waɗanda suka fi cancanta su wakilci jama’a a majalisa.
A halin yanzu dai, ana ci gaba da fatan cewa Hon. Abubakar Wada Nas Funtua zai amsa wannan kira na al’umma, tare da shiga fafatawar siyasa domin cika burin jama’ar Funtua
Musamman idan muka dubi yadda matashin yake da gogewa sosai ga al’amuran siyasa da kuma yadda yake taka rawar gani wajan tallafama rayuwar matasa ta bangarori daban daban musamman ban’garen samar da aiyukanyi.