Daily Gazette

Doguwa da Shuwaki Sun Yi Alhinin Rasuwar Jami’in NSCDC Bayan Taron Tallafin Azumi a Tudun-Wada

Doguwa da Shuwaki Sun Yi Alhinin Rasuwar Jami’in NSCDC Bayan Taron Tallafin Azumi a Tudun-Wada

 

Jagoran siyasar Doguwa/Tudun-Wada kuma ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana alhini da jimami kan rasuwar wani jami’in sa-kai na Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) mai suna Buhari, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Tudun-Wada, wanda ya rasu bayan wani lamari mai tayar da hankali da ya faru a wajen rabon tallafin azumi.

Lamarin ya faru ne bayan kammala taron rabon kayan abinci da kuɗaɗe da aka shirya domin tallafa wa al’ummar Tudun-Wada wajen sauƙaƙa musu gudanar da ibadar azumi da kuma shirye-shiryen bikin Sallah.

Rahotanni sun nuna cewa wasu matasa ɓata-gari sun tayar da tarzoma a wajen da nufin kwace wasu kuɗaɗen da aka raba wa al’umma. A yayin da jami’an tsaro da masu sa-kai ke ƙoƙarin dakile wannan mummunan aiki tare da kare jama’a, ne jami’in NSCDC ya samu munanan raunuka wanda daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.

An kuma bayyana cewa wannan lamari ya faru ne bayan Jagoran siyasar yankin, Doguwa, ya bar wurin taron tare da ɗan majalisar jihar Kano mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Tudun-Wada, Sule Lawan Shuwaki.

Doguwa ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyalan mamacin, abokan aikinsa da kuma daukacin al’ummar Tudun-Wada baki ɗaya. Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su tsananta bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki tare da tabbatar da an hukunta su bisa doka.

Ya kuma yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, tare da bai wa iyalansa, ‘yan uwansa da al’ummar yankin haƙurin jure wannan babban rashi. 🤲🕊️

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top