Daily Gazette

Shugaban  Hukumar Jin Daɗin Alhazan Kano Ya Zagaya Tanti Zuwa Tanti Domin Tabbatar da Walwalar Alhazai a Mina

Shugaban  Hukumar Jin Daɗin Alhazan Kano Ya Zagaya Tanti Zuwa Tanti Domin Tabbatar da Walwalar Alhazai a Mina

Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Abubakar Matawalle, ya gudanar da rangadin duba alhazan jihar da ke Mina, inda ya rika zagayawa tanti zuwa tanti domin tabbatar da cewa babu wata matsala da ke addabar alhazan yayin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
A yayin rangadin, Darakta Janar ɗin ya gana kai tsaye da alhazai, ya saurari koke-kokensu da shawarwarinsu tare da ba jami’an hukumar umarnin gaggauta magance duk wata matsala da aka lura da ita.
Alhaji Ibrahim Abubakar Matawalle ya bayyana cewa jin daɗi da walwalar alhazan Kano na daga cikin manyan abubuwan da hukumar ta sanya a gaba, yana mai jaddada cewa gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta ba da muhimmanci sosai ga nasarar aikin Hajji da kuma jin daɗin alhazan jihar a ƙasa mai tsarki.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da sanya ido a kan dukkan ayyukan da suka shafi masauki, abinci, sufuri da kuma kula da lafiyar alhazai domin tabbatar da cewa suna gudanar da ibadunsu cikin kwanciyar hankali da natsuwa.
Darakta Janar ɗin ya kuma yaba da haƙuri da biyayyar da alhazan Kano ke nunawa tare da ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da bin dokoki da ƙa’idojin aikin Hajji tare da mayar da hankali wajen gudanar da ibadunsu da kuma yi wa Jihar Kano da Najeriya addu’o’in zaman lafiya da ci gaba.
Wasu daga cikin alhazan da suka tattauna da Darakta Janar ɗin sun nuna jin daɗinsu kan wannan ziyara ta kai tsaye, inda suka bayyana cewa hakan ya nuna kulawa da jajircewar shugabannin hukumar wajen tabbatar da jin daɗinsu a Mina.
Sun kuma yabawa Gwamnan Jihar Kano da Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kano bisa shirye-shiryen da suka tanada domin sauƙaƙa wa alhazan gudanar da ibadunsu a wurare masu tsarki.
Rangadin na daga cikin matakan sa ido da Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kano ke aiwatarwa domin tabbatar da cewa dukkan alhazan jihar sun samu kulawar da ta dace da kuma gudanar da aikin Hajji cikin nasara.
Bayanin Hoto: Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Abubakar Matawalle, yayin da yake zagayawa tanti zuwa tanti a Mina domin duba halin da alhazan Kano ke ciki da tabbatar da cewa babu wata matsala da ke damunsu a yayin gudanar da aikin Hajjin 2026.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top