Ci gaban Karamar Hukumar Tudunwada: Kamsiloli Biyar Sun Ziyarci Doguwa a Abuja
Daga Sumayya Ahamad Ya’u

Hon. Alhassan Ado Doguwa Danmajalisa mai wakiltar Doguwa da Tudun-Wada ya karbi bakuncin wasu kamsiloli biyar daga karamar hukumar Tudunwada a birnin Abuja, a wata ziyara da aka bayyana cewa ta mayar da hankali kan bunkasa yankin da inganta rayuwar al’umma.
Kamsilolin sun ce zuwansu na daga cikin kokarin karfafa hadin kai da tattauna muhimman hanyoyin da za su taimaka wajen samar da ci gaba mai dorewa a Tudunwada. Sun kuma jaddada cikakken goyon bayansu ga Hon. Doguwa bisa irin jagoranci da yake nunawa.
Kamsilolin da suka halarci ziyarar tare da mazabunsu sun hada da:
Jibirin Abubakar — Malabar Shuwaki
Murtala Kabiru Dalauda — Mazabar Tsohon Gari
Abubakar Musa Kore — Mazabar Sabon Gari
Alh. Basiru Yalwa — Mazabar Jita
Abubakar Muhammad (Buba) —Mazabar Jandutse
Sun kara da cewa hadin gwiwa da Doguwa zai taimaka wajen samar da ayyukan raya kasa da inganta walwalar jama’a a yankin Tudunwada.
A nasa bangaren, Hon. Doguwa ya gode musu bisa wannan ziyara, yana mai cewa hakan na nuna kishin yankin da kuma aniyar kawo ci gaba. Ya kuma tabbatar da kudurinsa na ci gaba da aiki tukuru domin ganin an samu ci gaba mai ma’ana a Tudunwada.
Masu lura da harkokin siyasa sun bayyana wannan ziyara a matsayin wata alama ta karuwar hadin kai tsakanin shugabanni, wanda ka iya haifar da ci gaba mai anfani ga al’ummar yankin.