Daily Gazette

Doguwa Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Jami’in Civil Defence, Ya Nemi A Gaggauta Bincike Kan Tashin Hankali a Tudun Wada

Doguwa Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Jami’in Civil Defence, Ya Nemi A Gaggauta Bincike Kan Tashin Hankali a Tudun Wada

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana alhini tare da miƙa saƙon ta’aziyya bisa rasuwar wani jami’in tsaro na Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) wanda ya rasa ransa sakamakon wani tashin hankali da ya faru bayan rabon tallafin kayan azumi da na Sallah a Ƙaramar Hukumar Tudun Wada.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 13 ga Maris, 2026, Doguwa ya ce lamarin ya faru ne bayan kammala taron da aka shirya domin rabon kayan tallafi da kuɗaɗe ga al’ummar yankin maza da mata, domin sauƙaƙa musu gudanar da ibadar azumi da kuma shirye-shiryen bikin Sallah.

Ya bayyana cewa daga bisani ya samu rahoton cewa wasu ɓata-gari sun yi yunƙurin tayar da tarzoma a wurin rabon kayan, lamarin da ya yi sanadin rasuwar jami’in tsaron.

Doguwa ya miƙa ta’aziyyarsa ga hukumar Civil Defence, iyalan mamacin da kuma daukacin al’ummar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada, yana addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa tare da sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. 🤲

Hakazalika, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka haddasa tashin hankalin tare da ɗaukar matakin doka a kansu.

A ƙarshe, ɗan majalisar ya ja hankalin masu yaɗa labaran ƙarya da kalaman batanci da ke ƙoƙarin alakanta shi kai tsaye da abin da ya faru, inda ya ce za su ɗauki dukkan matakan doka da suka dace domin kare mutuncinsa da na al’ummar ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada. 📰

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top