Daily Gazette

Jagora Alhaji Nafiu Tukur Karaye Ya Nesanta kansa da wani Asusun Facebook na Bogi

Jagora Alhaji Nafiu Tukur Karaye Ya Gargadi Al’umma Kan Asusun Facebook na Bogi

 

Jagora kuma Mai gida  Alhaji Nafiu Tukur Karaye, ya ja hankalin al’umma da su yi taka-tsantsan biyo bayan gano wani asusun Facebook na bogi da aka buɗe da sunan “Nafi U Tukur Karaye”, wanda bai da wata alaƙa da shi.

Wannan na ƙunshe ne a cikin sanarwar gaggawa da Amadadin Jagora, Sulaiman Abdullahi Isah, ya fitar, inda ya bayyana cewa asusun da ake yadawa ba na gaskiya ba ne, kuma ana iya amfani da shi wajen yaudarar jama’a ko cutar da sunan Jagora.

Sanarwar ta jaddada cewa asusun Facebook na gaskiya guda ɗaya tilo da Alhaji Nafiu Tukur Karaye ke amfani da shi shi ne mai suna “Nafiu Karaye”, tare da roƙon al’umma da su guji mu’amala, karɓar saƙo ko amsa duk wani kira daga asusun bogin.

Hakazalika, sanarwar ta shawarci duk wanda ke da hannu wajen buɗe ko sarrafa wannan asusu na bogi da ya gaggauta bayyana kansa, kafin hukumomin tsaro—musamman Hukumar DSS—su ɗauki matakin da ya dace a kansa bisa doka.

Alhaji Nafiu Tukur Karaye ya nuna godiya ga al’umma bisa fahimta da haɗin kai, tare da kira da su ci gaba da bai wa hukumomi haɗin kai domin kare mutunci da tsaron jama’a a kafafen sada zumunta.

Sanarwar ta ƙare da jaddada aniyar Jagora na ci gaba da hulɗa ta gaskiya da jama’a ta hanyoyin da aka amince da su kawai.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top