Alamomin Sake Dawowar Acaba na bullowa a Kwaryar birnin Kano

Da alama dai sana’ar acaba wato daukar mutane a babur a matsayin haya na kokarin dawowa a cikin birnin Kano, duba da Yadda bayyanar masu babura ke kara yawaita dauke da mutane musamman da daddare .
Idan dai za a iya tunawa a shakarrar 2013 gwamnatin jihar Kano ta dakatar da sana’ar acaba a kwaryar birnin Kano saboda dalilan da ta bayyana na tsaro, biyo bayan amfani da babura da ake yi wajen aikata abubawan da ke da alaka da rashin tsaro. Hakan ya sanya mutane suka mayar da hankali wajen amfani da babur mai kafa uku wato adaidata sahu wajen zirga -zirga. Daga baya bincike ya nuna cewa ana amfani da shi kansa adaidaita sahun musamman da daddare, nan ma gwamnatin lokacin ta dakatar da amfani da adaidaita sahun da zarar karfe 10 na dare ta yi.
Amma a ‘yan kwanakin nan sai ga bayyanar masu sana’are acaba na kara yawa a cikin kwaryar birnin Kano
A watannin baya ga duk wanda yake kaiwa dare a Cikin Kano musamman a banagaren Nasarwa GRA , zai rinka ganin masu babura irin na zamani wanda aka fi sani da roba-roba suna ta zirga -zirga da goyo , wanda bincikenmu ya tabbatar mana da cewa Acaba suke yi a tsakanin Otel -Otel da kuma wasu unguwanni.
Bunciken Daily Gazette Hausa ya tabbatar da cewa a wannan dare irin wadanda suke gudanar da wannan acaba ta dare suna samun kudi masu yawa, Hasalima wasu daga cikin Fasinjojinsu musamman ‘yan mata suna da lambar wayarsu mafiyawan lokuta suna kiransu ne kawai su kai su inda suke bukata komai dare.
Bayyanar masu babura kirar Boxer da yawaitarsu shi ya ja hankalinmu muka yi bincike sosai inda muka gano cewa da zarar masu Adaidaita sahu sun tashi wato bayan karfe goma na dare har zuwa karfe 3 zuwa 4 tofa wadannan masu babura ne suke cin kasuwarsu.
Tun suna yawo su kadai sai dai ka tsayar da su har ta kai yanzu suna zama su taru a guri guda kamar dai lokacin da ake sana’ar acaba. Ga duk Wanda yake dadewa a waje babu shakka zai lura da tarin wadannan masu babura a kan Ahamdu Bello Way da Bompai Road Bakin Central Hotel da kuma kan Gadar Kabuga da dadai Sauran sassa na cikin birni.
Kuma fa a wannan lokaci akwai shingayen bincike na ‘yansanda a gurare da dama a cikin birnin Kano amma hakan bai hana wadannan ‘yan acaba na dare hada-hadarsu ba duk da cewa zuwa yanzu babu bayanin cewa gwamnati ta janye Dokar hana acaba.
Tambayar da muka yi wa kakakin Rundunar ‘yansanda ta jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa kan Shin hukumar ‘yansanda ta lura da dawowar masu Acaba, kuma dokar Hana Acaba tana nan?
Amma Allah bai sa hakanmu ya command ruwa ba, saboda matsalar ntwk bai sa ya ji abinda mu ke tambayaba . Ko ma dai menene aciki akwai bukatar mahukunta su sanya idanu domin ganin yadda wannan sana’a ta acaba da ke shirin Dawowa kuma musamman da daddare. Za mu cigaba da bibiya da kuma kawo muku irin yadda da matakan da ya kamata a dauka akan lamarin.