Daily Gazette

Auwal Aliyu Ya Zama Farfesa (Dan Arewa) Mafi Karancin Shekaru A Fannin Injiniyan Sinadarai

Auwal Aliyu Ya Zama Farfesa (Dan Arewa) Mafi Karancin Shekaru A Fannin Injiniyan Sinadarai

 

Farfesa Auwal Aliyu,ya zama Farfesa a Sashen Injiniyan Sinadarai na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya.

 

Tafiyar iliminsa labari ne na jajircewa, gogewa daga ƙasashen waje, da hidima ga Nijeriya.

 

Farfesa Auwal ya fara karatunsa na gaba da sakandire a kasar Rasha (Russia) ta hanyar tallafin karatu na Bilateral Educational Agreement (BEA).

Ya fara da koyon harshen Rashanci (Russian language) a makarantar D.I. Mendeleev Institute of Petrochemical Engineering, sannan ya ci gaba da samun digirinsa na farko da na biyu a fannin Injiniyan Sinadarai da Kimiyyar Halittu (Biotechnology) a Moscow Academy of Fine Chemical Technology.

 

Bayan nan ya kuma samu wani digirin na biyu a fannin Harkokin Kasa da Kasa da Diflomasiyya daga ABU a shekara ta 2011.

 

bayan Ya dawo Najeriya inda ya sami gagarumar tallafin karatun digirin digirgir (PhD) daga asusun Petroleum Technology Development Fund (PTDF).

Ya kuma yi wata ƙarin shaidar ƙwarewa a Birtaniya a fannin koyarwa a matakin manyan makarantu, wanda ya sa aka bashi shi a matsayin na6an kungiyar Fellow of the British Higher Education Academy a 2012.

 

A Jami’ar ABU, Farfesa Auwal ya taka muhimmiyar rawa wajen horar da ma’aikatan bincike na farko da za su yi aiki a matatar mai ta Dangote da kuma wasu matatun mai na ƙasashen waje.

 

Haka nan ya taba zama a matsayin mai bada shawara ga hukumar Raw Materials and Development Council (RMDC) dake Abuja, inda yake taimakawa ci gaban ƙasa ta hanyar bincike da goyon bayan

fasaha.

 

Bincikensa ya kai shi zuwa sassa daban-daban na duniya — inda ya gabatar da ayyukansa a taruka a ƙasashe kamar Netherlands, Faransa, Scotland, Amurka, da Oman.

 

Ya wallafa bincikensa a fitattun mujallu na duniya kamar su Fuel, Bioresource Technology Reports, Chemical Engineering Journal Advances, da Journal of Environmental Chemical Engineering.

 

Farfesa Auwal ya ƙirƙira kuma ya gwada wata na’urar kimiyya ta musamman domin nazarin sinadarai a cibiyar Russian Academy of Sciences dake Moscow. A halin yanzu, bincikensa yana mayar da hankali ne kan makomar makamashin Najeriya — musamman canjin daga amfani da man fetur zuwa makamashi daga sinadaran halitta da sabbin hanyoyin samar da makamashi mai tsafta.

 

Farfesa Auwal mamba ne a ƙungiyoyin ƙwararru na ƙasa da ƙasa irinsu American Institute of Chemical Engineers, Institution of Chemical Engineers UK, da Association of Energy Engineers USA.

 

Farfesa Auwal Aliyu ba wai kawai yana alfahari da iyalinsa ba ne, har ma yana bayar da gagarumar gudunmawa ga kimiyya, ilimi da ci gaban ƙasa baki ɗaya.

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top